Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Arsenal ta doke Burnley, yayin da United ta sha da ƙyar
Arsenal ta kamo Manchester City a mataki na ɗaya a teburin Premier bayan da ta doke Burnley da ci 3-1 a filin wasan Emirates .
Leandro Trossard ya fara zura ƙwallo a ragar Burnley bayan minti 45 da take was amma Josh Brownhill ya farkewa Burnley minti takwas bayan an dawo daga hutun rabin lokaci.
Bayan minti uku kacal William Saliba ya ci wa a Arsenal ƙwallo ta biyu kafin Oleksandr Zinchenko ya kammala zura ƙwallo ta uku a wasan a minti na 74.
Arsenal ta kammala wasan ne da ‘yan wasa 10 bayan da aka bai wa Fabio Vieira - wanda ya shigo wasan bayan hutun rabin lokaci - jan kati kai tsaye bayan da ya taka Brownhill.
A filin wasan Old trafford kuwa Manchester United ta samu nasarar da take buƙata a kan Luton a Old Trafford don rage matsin lamba kan kocinta Erik Ten Hag.
Ɗan wasan Sweden Victor Lindelof ne ya ci wa United ƙwallo ɗaya tilo a wasan a minti na 59, wadda ita ce ta taimaka wa United samun nasara a wasan.
Yanzu United tana mataki na 7 a teburin Premier na bana.