Real Madrid ta haƙura da Hernandez, Man City na son Wirtz da Guimaraes

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 2

Real Madrid ta janye daga zawarcin ɗan wasan bayan AC Milan Theo Hernandez, mai shekara 27, wanda hakan ya ƙara wa Manchester United ƙwarin gwiwar neman ɗaukar ɗan wasan na Faransa. (Fichajes)

Ɗan wasan Bayer Leverkusen da Jamus Florian Wirtz, mai shekara 21, da kuma ɗan wasan tsakiya na Newcastle United da Brazil Bruno Guimaraes, mai shekara 27, sun kasance kan gaba a jerin ƴan wasan da Manchester City ke sha'awa. (Times)

Za kuma a mara wa kocin Man City Pep Guardiola baya wurin fafutukar ɗaukar ɗan wasan tsakiyar Real Sociedad da Sifaniya Martin Zubimendi mai shekara 25. (ESPN)

Chelsea da Liverpool na shirin gogayya kan ɗan wasan baya Milos Kerkez, mai shekara 21, amma Bournemouth za ta yi iya ƙoƙarinta wurin ganin ta ci gaba da riƙe ɗan wasan na Serbia. (Football Insider)

Mikel Arteta na son ƙara dan wasan Juventus da Serbia Dusan Vlahovic, mai shekara 24, cikin tawagarsa ta Arsenal a watan Junairu. (Caught Offside)

RB Leipzig na son ɗaukar ɗan wasan Paris St-Germain da Holland Xavi Simons, mai shekara 21, kan kwantiragin dindindin, amma tana fuskantar hamayya daga Liverpool. (Caught Offside)

Manchester United za ta iya sallamar ɗan wasan tsakiyar Denmark Christian Eriksen, mai shekara 32 a watan Janairu idan ta samu wami tayi mai armashi a kansa. (Florian Plettenberg)

Wata ƙungiya da ke ƙarƙashin jagorancin Dan Friedkin na gab da ƙulla yarjejeniyar sayen Everton, inda ake sa ran kammala cinikin a mako mai zuwa. (Times)

Ba tunanin za a kori kocin Everton Sean Dyche nan da nan bayan ƙungiyar ta Friedkin ta karɓi ragamar kulob ɗin. (Football Insider)

Tottenham ba ta niyyar riƙe ɗan wasan gaba na Jamus Timo Werner, mai shekara 28, daga RB Leipzig kan kwantiragin dindindin a ƙarshen kakar wasa ta bana. (GiveMeSport)

Bournemouth na son ƙulla sabuwar yarjejeniya da kocinta Andoni Iraola saboda fargabar da ta ke yi cewa wasu ƙungiyoyin Premier na iya zawarcin kocin ɗan ƙasar Sifaniya. (TBR Football)

Gary O'Neil yana buƙatar nasara a wasan ranar Asabar da Ipswich Town samun damar ci gaba da riƙe muƙaminsa na kocin Wolves. (Football Insider)