Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Yanzu ne zan nuna ƙwarewata - Guardiola
Kocin Manchester City Pep Guardiola ya ce yana son ya nuna kwarewarsa ta hanyar fito da ƙungiyar daga koma bayan da take fuskanta.
City da za ta je Anfield domin wasa da Liverpool ta yi rashin nasara a wawsanni biyar da ta buga a jere a duka gasanni, har da wasan da ta ci 3-0 a Feyernoord a Champions a ranar Talata.
Indan suka yi rashin nasara a wasan zaia zama maki 11 ne tsakaninsu da kungiyar ta Arne Slot a teburin Premier.
Guardiola ya ce halin da ake ciki a yanzu ba na gaske ba ne, idan aka yi la'akari da sauran lokacin da ake da shi na ƙammala gasa.
Amma yanzu yana son ya mayar da hanakali kan yadda zai magance matsalar da yake fuskanta a ƙungiyar, maimakon magana a kan kofina 18 da ya lashe a City.
"Ba dadi amma me kake tsammani? kana zaton komai zai tafi daidai ne?" in ji shi.
"Da sauƙi abin idan ana maganar yadda kake lashe wasa 10 zuwa 12 a jere, kowanne cikinsu yana da kan ganiya, shekarunsu ba sa wuce 26,27 zuwa 28. Lokacin da komai yake tafiya a hakan komai sauki ne da shi.
"Yanzu ne zan nuna kaina."
Jin Guardiola na wannan kalamai abu ne mai tada hankali ga kokarin City.
Ko shakka babu tsohon kocin na Barcelona da Bayern shi ne koci mafi kwarewa a lokacinsa. A wajen wasu shi ne koci mafi kwarewa a tarihi.
"Cikin dogon lokaci shekara tara 10 zuwa 11 ka zauna a ƙungiyar cikin jin dadi," in ji shi
"Mun yi rashin nasara a wasa biyar, mun yi canjaras a wasa ɗaya da ya kamata mu ci, amma hakan na faruwa a kwallon kafa a mafi yawan lokaci.
"Ya kamata na yarda da halin da na tsinci kaina ciki. Babu ƙorafi ko zargin wani ko kuma cewa wani ne ya ja. Bai kamata mu gujewa aikinmu ba. Na ɗauki nauyin komai a kafaɗa ta.