Man City ta yi wasa na 30 a jere ba a doke ta ba a Premier League

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Manchester City ta yi nasara a kan Fulham 3-2 ranar Asabar a wasan mako na bakwai a Premier League a Etihad.

Wasa na 30 kenan a Premier League a jere ba a doke City ba, tun bayan nasarar da Aston Villa ta yi a kanta a cikin Disambar 2023.

Hakan ya sa ta yi kan-kan-kan da irin wannan bajintar da City ta yi tsakanin Afirilun 2017 zuwa Janairun 2018.

City na fatan kafa sabon tarihin wasa 31 a jere ba tare da rashin nasara ba a ranar 20 ga watan Oktoba a wasa da Wolverhampton a Premier League.

Arsenal ce kan gaba a tarihin wasa 49 a jere ba tare da rashin nasara ba a Premier League tsakanin Mayun 2003 zuwa Oktoban 2004.

Cikin karawa 30, City ta yi nasarar lashe 24 da cin ƙwallo 77, wadda ta lashe kofin Premier League a bara na huɗu a jere.

Haka kuma City ta yi karawa 50 a dukkan karawa ba tare da rashin nasara ba, tun bayan da Brentford ta doke ta a Nuwambar 2022, ta ci wasa 41 da canjaras tara.

Wasan da City ta buga da Real Madrid, an barshi a canjaras a Etihad a Champions League, saboda a bugun fenariti aka yi waje da City a gasar.

Kawo yanzu Pep Guardiola ya ja ragamar karawa 310 da yin nasara 229 da samun maki 730, haka kuma kociyan ya fara kakar bana da kafar dama.

City ta ci wasa biyar da canjaras biyu, wadda ke fatan lashe Premier League na 11 jimilla.

Ranar Asabar kociyan Fulham, Marco Silva ya yi rashin nasara ta 11 a hannun City, yayin da Guardiola ya yi nasara ta 12 a kan Fulham.

City tana ta biyu a kan teburin Premier League da tazarar maki ɗaya tsakani da Liverpool mai 18, baya karawa bakwai a babbar gasar tamaula ta Ingila ta bana.

Arsenal ce ta ukun teburi, mai maki iri ɗaya da na City mai 17.