Waiwaye: Girka shinkafa dafa-duka mafi yawa a duniya da ganawar Peter Obi da Obasanjo

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 6

A makon jiya ne Kundin bajinta na 'Guinness World Records' ya tabbatar cewa matashiyar nan yar Najeriya Hilda Baci ta kafa tarihin girka dafa-dukar shinkafa mafi yawa a duniya.

Hakan na zuwa ne bayan dubban mutane sun taru a ranar Juma'a 12 ga watan Satumban 2025 a birnin Legas, domin kallon yadda mai riƙe da kambin kundin bajintar kan girki ta gudanar da girkin shinkafa dafa-duka.

Dafa-dukar shinkafa da ake yi wa laƙabi da 'jollof' abinci ne da ya shahara a ƙasashen Najeriya da Ghana da Senegal da Saliyo da Laberiya da ma wasu da dama.

Hilda mai shekara 28 a duniya ta yi shuhura ne a shekara ta 2023 bayan kafa tarihin kwashe lokaci mafi tsawo tana girki ita kaɗai, na tsawon sa'a 93 da minti 11.

'Dole ne malamai su miƙa takardun huɗuba domin samun amincewar gwamnati'

Haka kuma a makon ne Gwamna Umar Bago na Jihar Neja ya bayyana cewa wajibi ne a kan masu wa'azi su riƙa miƙa takardun huɗubarsu domin samun amincewar gwamnati kafin su yi wa'azi a jihar.

Gwanan ya faɗi hakan ne a cikin wani shiri na gidan talabijin TVC inda ya fayyace wasu abubuwa na dokar da ke kokarin tsara yadda ake wa'azi a jihar.

Gwamnan ya ce, "Ban haramta wa'azi ba, Duk wanda zai yi huɗuba a ranar Juma'a, ya kamata ya kawo takardar da zai yi amfani da shi domin a duba abun da ke ciki, ko a Saudiya ma ana yin hakan."

"Ba za mu ce saboda an ba ka dama ka zama malami, za ka fita ka yi wa'azi wanda zai saɓawa mutane ko gwamnati ba." gwamnan ya ƙara da cewa.

"Saboda haka ne muke son mu ga abin da takardar wa'azin ya ƙunsa, abin da za a faɗi kuma muna aiki tare da hukumomin tsaro na DSS da ƴan sanda da NSCDC da sojoji." in ji gwamnan.

Wannan mataki da aka fara bayyanata ga bainar jama'a a farkon watan nan ya janyo ce-ce-ku-ce.

Peter Obi ya gana da Obasanjo da Ladoja gabanin zaɓen 2027

Wani labari da ya ɗauki hankali shi ne ɗan takarar jam'iyyar Labour a zaɓen 2023, Peter Obi, ya gana da tsohon shugaban ƙasa, Olusegun Obasanjo, gabanin zaɓen shugaban ƙasa na 2027.

Obi ya kuma ziyarci wanda aka naɗa a matsayin Olubadan, Rashidi Ladoja, a Jihar Oyo.

A wata sanarwa da ya fitar a shafinsa na X, Obi ya ce burinsa na ziyartar Ladoja shine don girmama shi saboda muhimmancin Ibadan a siyasa da zamantakewa da tattalin arzikin Najeriya.

Obi ya bayyana cewa Ladoja zai kawo ƙwarewarsa a matsayin tsohon sanata da gwamna da attajiri wajen jagorantar Ibadan zuwa matsayi mai daraja.

Obi ya ƙara da cewa, "Ziyarar duka mutanen biyu nan na da nasaba da ci gaban Najeriya da shugabanci na gaskiya da shugabanci da ke da niyyar sauya al'umma"

Ƴanbindiga sun yi garkuwa da mutum 40 a masallacin Zamfara

Aƙalla mutum 40 ne ake zargin ƴanbindiga suka sace daga wani masallaci da ke ƙauyen Gidan Turbe, ƙaramar hukumar Tsafe ta Jihar Zamfara, da safiyar Litinin ɗin makon na jiya a lokacin sallar asuba, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Majiyoyi sun ce an yi awon gaba da masallatan ne zuwa dazukan Gohori da ke yankin Tsafe.

A wani ɓangare kuma, rundunar Operation Hadarin Daji ta ce dakarunta sun gudanar da samame a jihohin arewa maso yamma, inda suka tarwatsa harin ƴan bindiga a Katsina, da kuma daƙile wani harin da aka kai wa jami'an NSCDC a kusa da dajin Danmusa.

Ƴanbindiga sun yi wa hakimi yankan rago a Zamfara

Haka kuma a farkon makon ne wasu ƴanbindga ɗauke da makamai sun auka wa garin Dogon Daji da ke yankin ƙaramar hukumar Tsafe a jihar Zamfara, tare da yi wa hakimin garin yankan rago.

Shugaban ƙaramar hukumar Tsafe Hon. Garba Shehu Tsafe ya tabbatar wa BBC cewa lamarin ya faru ne a yau Litinin da maraice.

''Yanzu-yanzu muka samun rahoton cewa ƴanbindiga sun shiga garin Dogon Daji na Nasarawar Keta, sun kuma yanka hakimin garin'', in ji shi.

Ya ƙara da cewa a wunin yau ƴanbindigar sun tare wasu hanyoyi a yankin da ke kai wa zuwa Gusau.

Shugaban ƙaramar hukumar ya alaƙanta ƙaruwar hare-haren yankin da sluhun da ake yi a jihar Katsina mai makwabtaka.

Dama dai masana tsaro sun jima suna gargaɗin cewa yin sulhu da ƴanbindigar ba mafita ba ce, saboda za su iya barin wurin da aka yi sulhu da su domin kai hari wasu yankunan, sannan su dawo wurin da aka yi sulhun domin samun mafaka.

Sojojin Najeriya sun ce sun kashe mayaƙan ISWAP 11

A can jihar Borno ma, an samu labari a cikin makon, inda rundunar sojin Najeriya ta ce ta kashe aƙalla mayaƙan ISWAP 11 a farmakin da ta kai jihohin Borno da Adamawa.

Cikin wata sanarwa da rundunar haɗin gwiwa da ke yaƙi da mayaƙan Boko Haram da ISWAP a yankin arewa maso gabashin Najeriya, ta fitar a yau Talata ta ce ta yi nasarar kashe mayaƙan na ISWAP a wani artabu a hanyar Baga da ke jihar Borno da kuma yankin Magagali a jihar Adamawa.

Sanarwar ta ce lamarin ya faru ne a jiya Litinin bayan da mayaƙan Iswap suka yi wa dakarun sojin kwanton ɓauna a kusa da Garin Giwa a ƙaramar hukumar Kukawa, inda suka dasa bom tare da buɗe wuta.

Amma sanarwar ta ce sojojin sun yi nasarar murƙushe harin tare da kashe mayaƙan ISWAP takwas ciki har da kwamandojojin ƙungiyar biyu, kuma sojojin sun yi nasarar kwato makamai da Babura a cewar sanarwar.

Haka kuma rundunar sojin ta Najeriya ta ce dakarunta tare da taimakon mafarauta da yan sakai sun kashe wasu ƙarin mayaƙan uku tare da karɓe makamansu a jihar Adamawa.

Sai dai sanarwar rundunar haɗin gwiwar ba ta bayyana ko an kashe sojojin ba a artabun. Najeriya ta daɗe tana fama da matsalar Boko Haram a arewa maso gabashi da kuma ISWAP da ta ɓalle daga ƙungiyar.

Gobara a Legas ta kashe ma'aikata 12 na FIRS da UBA

Haka kuma a makon, shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya nuna alhininsa dangane mutane 12 da suka rasa rayukansu a lokacin ibtila'in gobarar da ta tashi a dogon ginin Afritower a birnin Legas.

Gobarar wadda ta tashi da misalin ƙarfe 1 na daren ranar Talata ta shafi ginin hukumar tattara haraji ta FIRS da bankin UBA da kuma Capital UNited waɗanda dukkanninsu suke aiki a rukunin ginin.

Ofishin hukumar tattara haraji ta Najeriya, FIRS da ke Legas ya tabbatar da rasuwar ma'aikatan nasa sakamakon tashin gobarar..

A cikin wata sanarwar da ofisihin ya fitar a shafinsa na X, ya ce bayan tashin wutar ne sai ma'aikata suka rinƙa durowa daga ofishin da ke hawa na bakwai al'amarin da ya sa wasu suka rasu sannan wasu da dama suka samu raunuka.

Duk da cewa hukumar ba ta faɗi adadin mutanen da suka mutu ko jikkata ba amma rahotanni na cewa waɗanda suka mutu sun kai mutum huɗu.

Atiku ya ɗauki nauyin karatun ɗaliban Yobe da suka ci gasa a Birtaniya

Haka kuma tsohon mataimakin shugaban Najeriya kuma jagoran adawa Atiku Abubakar ya ɗauki nauyin karatun ɗalibai uku da suka yi nasara a gasar Turancin Ingilishi ta TeenEagle Global Finals a Ingila a cikin makon.

Wata sanarwa da Gidauniyar Atiku ta fitar mai kwanan watan 5 ga watan Agusta ta ce nasarar da Nafisa Abdullahi, da Rukaiya Mohammed Fema, da Khadija Kashim Kalli suka yi "shaida ce cewa kwane yaro na iya cim ma burika".

"Saboda karrama wannan bajinta taku, Gidauniyar Atiku Abubakar za ta ɗauki nauyin kammala karatun sakandare da kuma na duk jami'ar da kuka zaɓa," a cewar sanarwar da sakataren gidauniyar, Farfesa Ahmadu Shehu ya fitar.

A farkon watan Agusta ne matasan 'yan asalin jihar Yobe suka doke takwarorinsu 20,000 daga sassan duniya a gasar bayan sun wakilci Najeriya daga makarantar Tulip International College.

Cikin wani saƙo da ya wallafa a shafukan sada zumunta, Atiku ya ce a jiya Alhamis ne ɗaya daga cikinsu Nafisa Abdullahi ta kai masa ziyara a gidansa da ke Abuja, babban birnin Najeriya

Gwamnan Rivers Siminalayi Fubara ya koma bakin aiki yau Juma'a

Haka kuma a ranar Juma'a ce Gwamnan jihar Rivers, Siminalayi Fubara ya shiga fadar gwamnatin jihar, kwana ɗaya bayan shugaban Najeriya Bola Tinubu ya ɗage dokar ta-ɓaci da ya ƙaƙaba a jihar.

Fubara ya shiga gdan gwamnati ne tare da rakiyar mai ɗakinsa, Valerie Fubara da mataimakiyarsa Ngozi Nma Odu.

A lokacin da ya isa gidan gwamnati, Fubara ya shaida wa dandazon mutanen da suka taru domin tarbarsa cewa "ƙaunar da kuka nuna min ta sa jikina ya yi sanyi."

Tun a ranar Laraba ne shugaban na Najeriya Bola Tinubu ya sanar da kawo ƙarshen dokar ta-ɓacin, inda ya ce "daga Alhamis 18 ga watan Satumba, Gwamna Siminalayi Fubara da mataimakiyarsa, Ngozi Nma Odu, da mambobin majalisar dokokin jihar ƙarƙashin jagoracin kakakin majalisar jihar, Martins Amaewhule, za su koma aikinsu''.

Hakan ya kawo ƙarshen dokar da ta shafe tsawon wata shida a jihar tun bayan da shugaban ya sanar da ita ranar 18 ga watan Maris ɗin 2025.

Sai dai rashin bayyanar Gwamna Fubara a gidan gwamnati jiya Alhamis ya haifar da raɗe-raɗi game da inda ya ke da kuma abin da ya hana shi komawa ofis.

Wasu da dama sun soki shugaban Najeriya Bola Tinubu kan dakatar da zaɓaɓɓen gwamnan jiha da kuma ƴan majalisa.

Sai dai shugaban ya ce ya yi hakan ne domin samun maslaha bayan turnuƙewar rikicin siyasa tsakanin Fubara da magabacinsa Nyesom Wike.