Liverpool ta tabbatar da matsayinta a saman teburi bayan ragargaje Tottenham har gida

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Liverpool ta ba da tazarar maki huɗu a saman teburin Premier League bayan ragargaje Tottehnam har gida da ci 6-3.

Tun ana minti na 23 da take wasan Liverpool ta samu damar zira ƙwallo daga kurosin ɗin da Alexander-Arnold ya yi zuwa Luis Diaz, sai Alexis Mac Allister ya ƙara ta biyu minti 13 bayan haka.

James Maddison ne ya fara farfaɗo da Spurs ɗin lokacin da ya farke ƙwallo minti huɗu kafin a tafi hutun rabin lokaci, amma kuma Szoboszlai ya ƙara ci wa Liverpool ana sauran 'yan mintuna kafin tafiya hutun.

Tottenhma da ke fama da masu jinya a tawagarta, sun nuna ɓaraka ƙarara a wasan, abin da ya jawo aka ci gaba da ɗura mata ƙwallayen.

A wasan ne kuma Mohamed Salah ya kamo Billy Liddell a yawan ƙwallayen da suka ci wa Liverpool na 228 bayan ya ci a minti na 54, kafin daga baya ya shiga jerin mutum huɗu da suka fi ci wa Liverpool ɗin ƙwallaye a tarihi da ƙwallon da ya ƙara.

Dejan Kulusevski ya ci wa Tottenham ƙwallonsa na biyar cikin wasa biyar a jere, yayin da Solanke ya kusa ɓata wa Liverpool wasa da tasa ƙwallon.

Daga baya dai Diaz ya ci ta biyu kuma ta shida ga masu ziyarar.

Sakamakon ya sa Tottenham ta koma ta 11 a teburi, kafin kuma ta ziyarci gidan Forest ranar Alhamis a wasan Premier mako na 18.