Gane Mini Hanya : Magance matsalar tsaro 01/03/2025

Bayanan sautiLatsa hoton sama domin sauraro
An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Wasu masana tsaro a Nijeriya sun yi kira ga hukumomin ƙasar, su canza salon yaƙi da ƴan fashin daji, saboda a cewarsu ga alama salon da ake bi yanzu ba ya tasirin da ake buƙata.

Sun ce yaƙi da ƴan fashin daji a yankin arewa maso yamma da ma wasu jihohin arewa ta tsakiya, zai fi nasara ne idan suka ƙarfafa al'amuran shugabanci nagari da samar da damarmakin inganta rayuwa ga matasa.

Birgediya Janar Sani Usman Kukasheka (mai ritaya) ya ce kamata ya yi jihohin da ke fama da rikicin ƴan fashin daji su ƙara haɗa kai a tsakaninsu kuma su riƙa aiki tare wajen tunkarar masu kai hare-hare da satar mutane don neman kuɗin fansa.