Wa zai maye gurbin Rodri a Man City?

Manchester City

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Kociyan Manchester City, Pep Guradiola ya ce Rodri zai yi jinya, mai tsawo, sakamakon raunin da ya ji a wasan Arsenal ranar Lahadi.

City ta tashi 2-2 da Gunners a wasan mako na biyar a Etihad a babbar gasar tamaula ta Ingila.

Har yanzu ba a sanar da kwanakin da zai yi jinya ba, City ta ce za a ci gaba da yi masa gwaje-gwaje don tantance raunin da ya ji a gwiwa.

Sai dai kociyan City na neman mafita, saboda rawa mai yawa da Rodri ke takawa a ƙungiyar, domin neman maye madadinsa kafin ya warke.

City ta yi rashin nasara kaso 11 cikin 100 tare da Rodri a cikin fili, idan aka kwatanta rashin nasara kaso 24 cikin 100 ba tare da ya buga mata wasa ba tun daga 2019 da ya fara yi mata tamaula.

City za ta duba daga cikin ƴan wasanta don maye gurbin Rodri da ya haɗa da Mateo Kovacic ko Ilkay Gundogan ko John Stones ko kuma Rico Lewis .

Amma idan Rodri zai yi jinya har zuwa sabuwar shekarar 2025, kenan City za ta bukaci ɗaukar ɗan wasa a watan Janairu.

City za ta kira Kalvin Philips daga wasannin aro da yake yi a Ipswich Town a watan Janairu, banda shi wa ya kamata ta nema madadin Rodri?

Wasu na cewar cikin wadanda za su iya maye gurbin Rodri sun haɗa da Declan Rice na Arsenal da Federico Valverde na Real Madrid - shin ƙungiyoyinsu za su yadda su rabu da su a Janairu?

Idan City ba ta samu taya waɗan nan ƴan wasan ba, waɗan ne ya kamata ta nema?