Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Man City ta kara cin karo da koma baya a wasa da Feyenoord
Manchester City da Feyenoord sun tashi 3-3 a wasa na biyar-biyar a Champions League da suka kara ranar Talata a Etihad.
City ta fara cin ƙwallo ta hannun Erling Haaland a bugun fenariti, haka suka je hutu an zura ƙwallo a ragar Feyenoord.
Bayan da suka koma zagaye na biyu ne Ilkay Gundogan ya kara na biyu, sannan Haaland ya kara na uku, sannan na biyu da ya ci a wasan.
Daga baya ne Feyenoord ta farke dukkan ukun saura minti 15 a tashi daga karawar ta hannun Hadj Moussa da Giménez da kuma Hancko.
Wannan shi ne karo na shida a jere da City ta yi karawa ba tare da nasara ba a dukkan fafatawa da rashin nasara biyar a jere.
Ranar Asabar Tottenham ta je ta doke City 4-0 a Etihad a Premier League karo na biyar da ta yi rashin nasara a jere a dukkan fafatawa.
Karon farko da Guardiola ya sha kashi a wasa biyar a jere, tun bayan da ya fara aikin horar da tamaula a tarihi.
Kuma karon farko da City ta yi rashin nasara biyar a jere tun bayan Afirilun 2006, kuma karo na uku a jere da aka doke ta a Premier League.
Da wannan sakamakon City mai maki 23 tana da tazarar maki takwas tsakaninta da Liverpool, wadda ke jan ragama, bayan cin Southampton 3-2 ranar Lahadi.
Ƙungiyar da ke Etihad na fama da masu jinya da suka haɗa da wanda ya lashe ƙyautar Ballon d'Or, Rodri da Ruben Dias da Mateo Kovacic.
Sauran sun haɗa da Jeremy Doku da kuma Oscar Bobb, yayin da Kevin de Bruyne ya murmure.
Guardiola, wanda ya saka hannu kan yarjejeniyar ci gaba da horar da tamaula a City kaka biyu, ya lashe kofi 18 a Etihad har da Premier League shida da Champions League.