Ba ƙaramin farashi ne zai sa na saki Toney ba - Thomas Frank

Asalin hoton, Getty images
Kocin Brentford, Thomas Frank ya ce ba "ƙaramin farashi" ba ne zai sa kulob ɗin ya saki ɗan wasan kulob din na gaba, Ivan Toney a wannan watan.
Bayanai dai na alaƙanta ƙungiyoyin wasan nan guda biyu masu adawa da juna na birnin London wato Arsenal da Chelsea da zawarcin ɗan wasan mai shekaru 27.
Mista Frank yana da ƙwarin gwiwa cewa ɗan wasan na gaba na Ingila zai ci gaba da zama a kulob ɗin har bayan kakar musayar 'yan wasa ta watan Janairu.
"Yar ƙaramar amsa da zan ba ki ita ce, E," in ji Frank, lokacin da aka tambaye shi ko Toney zai ci gaba da zama a kulob ɗin.
Ya ƙara da cewa " Ban da alaƙa da tattaunawa kan abin da za a biya, amma dai zan iya bayar da shawara cewa ya kamata a biya da yawa, idan ba haka ba zai ci gaba da zama a nan."
Brentford dai zai matukar son ɗan wasan wanda ya ci kwallaye 21 a kakar wasan da ta gabata, ya koma masa bayan rashin nasararsu a wasanni biyar da suka taka.
Yanzu dai Brentford na da maki 4 kacal ta faɗa ƙarƙashin tebur, a wasansu na uku a gasar.







