Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Super Eagles da Mozambique za su kara ranar Litinin
Tawagar kwallon kafa ta Najeriya za ta buga wasan sada zumunta da ta Mozambique ranar Litinin a Portugal.
Super Eagles ta tashi 2-2 da Saudia Arabia ranar Juma'a, a wani wasan sada zumunta da suka buga a Estadio Municipal de Portimao da ke Portugal.
Tuni dai Najeriya ta samu gurbin shiga gasar kofin nahiyar Afirka da za a yi a Ivory Coast a 2024, an kuma haɗa ta rukuni da mai masaukin baki.
Super Eagles na buga wasannin sada zumunta don gwada 'yan wasanta a shirin fafatawar neman gurbin shiga gasar kofin duniya da za ta buga da Lesotho da kuma Zimbabwe a cikin watan Nuwamba..
Ɗan wasa Kelechi Iheanacho, wanda ya ci Saudia Arabia kwallo ranar Juma'a ba zai buga karawar ta ranar Litin ba, wanda ya koma gida don magance matsala ta kashin kansa.
Haka kuma koci, Jose Peseiro ya sanar cewar Victor Osimhen bai zai buga karawar ba, sakamakon raunin da ya ji a fafatawa da Saudiyya.
Watakila Pesseiro ya maye gurbin Osimhen da ko dai Terem Moffi ko Victor Boniface ko Samuel Chukwueze ko Sadiq Umar ko kuma Moses Simon.
Masu tsaron baya Kenneth Omeruo da Jordan Torunarigha da Chidozie Awaziem da mai buga tsakiya Frank Onyeka da Fisayo Dele-Bashiru da kuma Raphael Onyedika ba su buga wasan Saudia Arabia ba, watakila su kara a ranar Litinin.