Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ina jin kunyar roƙon abinci - Mataimakin shugaban Kenya
Mataimakin shugaban ƙasar Kenya, Rigathi Gachagua, ya ce ya ji kunya saboda rokon taimakon abinci da ya yi a daidai lokacin da ake fama da ƙarancin abinci a faɗin ƙasar.
“Na shafe dukkan lokaci muna rokon abinci daga ƙasashen waje. Har da waɗanda suka yi mana mulkin mallaka. Sai dai bani da wani zaɓi saboda ba za mu bar mutanen mu su mutu ba,’’ in ji Rigathi Gachagua.
Mataimakin shugaban ƙasar ya ce ƙarancin ruwan sama da aka samu, ya jefa mutane da dama cikin rashin abinci, inda har ta kai ga wasu sun mutu.
Ya ce ya yi addu’a a kan tsaunin Kenya da ‘Allah ya kawowa ƙasar waraka’’ da kuma ceto mutane daga cikin matsalar ta ƙarancin abinci.
Da yake magana da wata kafar talabijin ta ƙasar, mista Gachagua, ya ce rokon abinci ba abu ne da aka san al’ummarsa da shi ba, inda ya kwatanta hakan da zubar da ƙima a matsayin sa na ɗa ga tsohon ɗan gwagwarmayar ƙare hakkin ɗan adam.
Kenya na daga cikin ƙasashen gabacin Afirka da ke fama da mummunan fari.
Wasu na ganin cewa wannan ne fari mafi muni da ƙasar ta fuskanta cikin shekaru masu dama.
Dabbobi da al'umma sun tagayyara, inda za ka iya ganin ƙasusuwan dabbobi waɗanda suka gaza a dazuka.