Bayanan da kuke nema kan tsarin karɓar kaya bashi da Tinubu ya ƙaddamar

Asalin hoton, State House
- Marubuci, Usman Minjibir
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Senior Journalist
- Aiko rahoto daga, Abuja, Najeriya
- An wallafa
Kamar sauran ƙasashen duniya da suka ci gaba irin su Amurka da Birtaniya - waɗanda ake yi wa kirari da ƙasashen cin bashi ko kuma 'credit countries' a Turance, - gwamnatin Najeriya na son dabbaƙa tsarin bai wa 'yan ƙasa kayan amfanin yau da kullum a matsayin bashi.
Sai dai tun bayan da Shugaban Ƙasar Bola Ahmed Tinubu ya ƙaddamar da tsarin na Consumer Credit Scheme ranar Laraba, 'yan ƙasar ke ta neman sanin yadda tsarin yake aiki da ma abin da yake nufi.
Harwayau, an yi ta yaɗa jita-jita da labarin ƙanzon-kurege cewa tsarin kuɗi ne na bulus ba bashi ba, inda da dama daga 'yan ƙasar ke ta rububin cike fam na karɓar ƙudin ba tare da sanin yadda za ta kaya ba.
Hakan ne ya sa BBC Hausa ta tuntuɓi masanan tattalin arziki da dama domin yin fashin baƙi.
Yadda tsarin karɓar kaya bashi yake
Domin masu bibiyarmu su fahimci yadda tsarin yake, mun fayyace shi ta wannan hanya:
- Tsari ne na bashi, ba kyauta ba.
- Idan mutum ya ga duk irin abin da yake so ya saya kuma ba shi da kuɗi a hannu sai ya cike fam ta adireshin hukumar bayar da bashin
- Hukumar ce za ta samar da kuɗin ta hanyar aiki da Babban Bankin Najeriya da ƙungiyoyin tsumi da tanadi
- Za a rinƙa cire kuɗin da kaɗan-kaɗan zuwa wani lokaci har mutum ya kammala biya
- Akwai kuɗin ruwa da wanda ake bi bashi zai rinƙa ɗorawa
- Sai kana da aikin-yi kafin ka cancanci shiga tsarin
- Yanzu za a fara da ma'aikatan gwamnati kafin sauran ma'aikata da ma sauran 'yan ƙasa
Mene ne alfanun tsarin?
Malam Yusha'u Aliyu masanin tattalin arziki ne a Abuja kuma ya shaida wa BBC cewa wannan tsari ne mai muhimmancin gaske domin tuntuni ya kamata Najeriya ta fara aiki da shi.
"Ai da ma irin wannan tsari ƙasashen da suka ci gaba a duniya suke bi, shi ya sa za ka ga kowa na iya mallakar abubuwan more rayuwa kamar gidan kansa, da mota, da kayan-ɗaki, da duk wani abin da ɗan'adam ke buƙata. A taƙaice dai wannan hanya ce ta rage ko kuma yaye baƙin talauci a ƙasa" In ji Malam Yusha'u.
Ya kuma ƙara da cewa "abu na biyu shi ne; tsari zai sa 'yan ƙasa su ƙara ƙaimi wajen samar da kayan da jama'ar ke bukata, wato za a samu yawaitar ƙere-ƙere da ƙirƙire-ƙirƙire a Najeriya".
Dangane da yawaitar ƙudi a hannun mutane, malam Yusha'u ya ce: "Wannan tsari zai taimaka sosai wajen rage yawaitar kuɗaɗe a hannun al'umma. Kuma hakan zai bai wa gwamnati damar shawo kan tashin farashin kayan da ake gani tun da babu kuɗi da yawa a hannun al'umma."
Ko tsarin na da matsaloli?
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Ita ma wnanan tambayar mun miƙa wa Malam Lawal Habib Yahaya, malami a sashen nazarin kuɗade na Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta jihar Kano. Ga kuma abin da ya ce:
"Tsari ne mai kyau ga ƙasashen da suka ci gaba, amma ba na tunanin tsarin zai yi kyau a Najeriya. Misali, nawa ne albashin ma'aikata a Najeriya? To ka ga kana fama da ƙarancin albashi kuma kana ɗaukar bashi? Ma'aikaci zai kasance a cikin bashi har ƙarshen rayuwarsa.
"Sannan kasancewar Najeriya a yanzu haka ba ta samar da kayan da take buƙata kamar yadda ƙasashen da ke amfani da wannan tsari ke yi, zai sa duk kayan da jama'a za su ɗauka bashi za a shigo da su ne daga ƙasashen waje. Kuma abin da hakan yake nufi shi ne ƙasar za ta zama matattarar kayan ƙasashen waje."
Wani abu mai alaƙa da batun kasancewar Najeriyar zama matattarar kayayyaki, shi ne na tilasta amfani da kudin ƙasashen waje musmaman dala.
"Yayin da ƙasa ba ta iya kera ko sana'anta abubuwan da 'yan ƙasar ke buƙata, to dole ne a yi amfani da dalar Amurka wajen siyo su a shigar da su Najeriya. Ka ga kenan an koma gidan jiya, wato a lokacin ne ma dalar za ta yi tashin gwauron zabi da ka iya jefa ƙasar cikin halin tsadar rayuwa." In ji Malam Lawal.
Kazalika, Malam lawal ya yi tsokaci kan kuɗin ruwa da ake sanyawa ga wanda ya ci bashin.
"Duk da cewa har yanzu hukumar da ke da alhakin tsarin ba ta yi cikakken bayani ba kan yawan kuɗin ruwan da za ta ɗora kan bashin, amma wani abu ne da idan ya yi yawa zai iya tagayyara tsarin tattalin arzikin mutane. Sannan kuma akwai mabiya addinin da ke ƙyamatar sa [kuɗin-ruwa."
Mafita
Duka masanan sun ce idan dai ana son tsarin ya yi tasirin da ake buƙata to sai an samar da wasu abubuwa biyar kamar haka:
- Wutar lantarki domin masana'antu su farfaɗo
- Samar wa al'ummar ƙasa aikin-yi domin samun sukuni na iya sayen abubuwa ko kuma su ɗauki bashi domin biya daga baya
- Bai wa ma'aikatan Najeriya isasshen albashi domin samun shiga shirin
- Rage yawan kuɗin-ruwa
- Fito da tsarin da ba shi da kuɗin ruwa domin janyo waɗanda ke ƙyamatar ruwa kamar wasu daga cikin Musulmi da Kirista









