Amad ba zai buga wa Ivory Coast wasa da Saliyo ba gida da waje

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Amad Diallo ya hakura ba zai buga wa Ivory Coast wasan neman shiga gasar kofin Afirka da Morocco za ta gudanar a 2025 ba, sakamakon rashin lafiya.

Tun farko an tsara cewar mai shekara 22 zai buga karawa da Saliyo a gida ranar 11 ga watan Oktoba.

Yayin da za a yi wasa na biyu a Saliyo ranar Talata 15 ga watan Oktoba, domin shiga babbar gasar tamaula ta Afirka da za a gudanar a shekara mai zuwa.

Amma ana sa ran zai yiwa Manchester United wasan Premier League da za ta kara da Brentford ranar Asabar 19 ga watan Oktoba a Old Trafford.

Amad ya fara buga wa kasarsa tamaula a 2021, wanda kawo yanzu ya yiwa Ivory Coast karawa shida jimilla.

Koci, Emerse Fae ne ya gayyaci Amad a watan Yuni, bayan wata 15 rabon da ya buga wa Ivory Coast tamaula.

Ivory Coast ta fara doke Zambia da Chad a wasan neman shiga gasar kofin Afirka, idan ta lashe wasa biyu da za ta yi da Saliyo, kenan ta samu tikiti kai tsaye da maki 12.

Morocco za ta gudanar da gasar cin kofin nahiyar Afirka a cikin Disambar 2025 zuwa Janairun 2026.

Sauran ƴan wasan Manchester United da ba za su buga wa kasashensu tamaula ba a lokacin nan ,sun haɗa da Alejandro Garnacho da Kobbie Mainoo da kuma Noussair Mazraoui.