Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Man City ta sayi Marmoush na Frankfurt fam miliyan 59
Manchester City ta sayi dan wasan gaba na Masar Omar Marmoush daga Eintracht Frankfurt a kan yro miliyan 70 (£59m).
Dan wasan mai shekara 25 ya amince da yarjejeniyar har zuwa watan Yuni na 2029 da sauran 'yan tsarabe-tsarabe da suka kai na fam miliyan 4.
Marmoush ya ci kwallo 15 a wasannin gasar Jamus, Bundesliga 17 a kakar nan, inda yake bin bayan kyaftin din Ingila Harry Kane na Bayern Munich wanda shi kuma ya zura kwallo 17 zuwa yanzu a gasar ta bana.
Marmoush ya bayyana jin dadinsa ta tafiyar da zai yi zuwa Manchester City, inda ya bayyana kungiyar da cewa tana daya daga cikin manyan kungiyoyin duniya a cikin shekara 10.
Ya ce shi da iyalinsa suna matukar murna da fadawar cinikin, kuma burinsa ne ya cika.