Amare 50 da aka haɗa bikinsu don rage kashe kuɗi a Afghanistan

Afghanistan

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Ana ƙara samun irin waɗannan bukukuwa da nufin rage yawan kuɗaɗe da ake kashewa lokacin aure
    • Marubuci, Daga Thomas Mackintosh
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News
  • An wallafa

An gudanar da wani gagarumin bikin aure na ma'aurata 50 a ƙasar Afganistan.

Irin waɗannan shagulgulan dai sun zama ruwan dare yayin da ma'aurata masu karamin karfi ke neman kaucewa yawan kashe kuɗi.

Sabbin amaren sun zauna wurare daban-daban a wajen da aka shirya bikin - inda bayan cin abincin rana suka fara fitowa, kamar yadda kafafen yaɗa labarai na ƙasar suka bayyana.

Wata ƙungiyar agaji ce ta shirya taron bikin wanda aka yi a birnin Kabul, ta kuma bai wa sabbin ma’auratan kayayyaki da suka haɗa da kafet da kayan amfanin gida don fara rayuwar aure.

Wani jami’in ma’aikatar kula da inganta nagarta ya yi jawabi a wajen taron bukukuwan.

An karanta karatun Kur'ani a wajen. Gwamnatin Taliban dai ta haramta rawa da waka a faɗin ƙasar tun bayan komawa kan karagar mulki a watan Agustan 2021.

Daga nan aka tafi da angwaye da kuma amaren cikin motoci da aka yi musu ado da launin kore da kuma jajayen robobi na alamar zuciya.

Roohullah Rezayi, mai shekaru 18, ya bayyanawa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa idan ba a taimaka wajen ɗaura musu auren ba, to da ba zai samu damar yi ba.

"Ɗaurin auren da aka saɓa zai iya lakume kuɗi akalla 200,000 zuwa 250,000 a kuɗin ƙasar, amma a wannan karon kuɗin ba zai haura 10,000 zuwa 15,000," in ji shi.

Matashin wanda ɗan kabilar Hazara na ƴan Shia marasa rinjaye. Ya fito ne daga lardin Ghor, yana samun 4,500 a kowace rana a kuɗin ƙasar daga ƴan aikace-aikace da yake yi, in ji hukumar.

“Mun gayyaci mutane 35 daga iyalan gidanmu guda biyu kaɗai, idan ba haka ba da sun kai 300 zuwa 400,” in ji shi.

Ga wasu daga cikin mutanen da suka zama angwaye, sun ɗauki tsawon lokaci suna iran ganin irin wannan rana, in ji AFP.

"Na shafe shekaru uku ina jiran wannan rana," in ji Samiullah Zamani, ɗan shekara 23, wanda manomi ne daga lardin Kabul. "Ba zan iya jiran ganin amariya ta ba."

Afghanistan

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Angwayen sun isa wurin shagalin gagarumin bikin da aka shirya musu ranar Litinin wanda aka yi a Kabul
Afghanistan

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, An ajiye sabbin amaren a wani wuri na daban - inda bayan cin abincin rana ne suka fara fitowa zuwa wajen bikin
Afghanistan

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Ƴan uwan angwaye da amaren sun halarci taron bikin da aka shirya a Kabul
Afghanistan

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, An haramta rawa da waka a Afghanistan tun bayan komawa kan mulki da Taliban ta yi