Robinho zai sha daurin shekara tara saboda laifin fyade

Asalin hoton, Getty Images
An sanar da tsohon dan kwallon Manchester City da Real Madrid, Robinho cewar zai yi zaman yari shekara tara a Brazil kan hukuncin laifin yin fyade.
An samu Robinho mai shekara 40 da laifi a wata kotu a Italiya a 2017, wanda yana cikin taron dangin fyaden da aka yi wa wata mata 'yar Albania 'yar shekara 22.
Dan kwallon yana zaune a Brazil, wanda ba a mika shi Italiya ba, to amma alkalai a Brazil sun yanke hukunci ranar Laraba cewar zai yi zaman yari a kasar kamar yadda Italiya ta bukata.
Lauyoyi sun ce yana da lokacin da zai daukaka kara kafin hukuncin ya fara aiki a kansa.
Tsohon dan wasan tawagar Brazil da ya buga wa kasar wasa 100, yana taka leda a AC Milan a lokacin da aka aikata laifin da aka zarge shi.
A shekarar 2020 aka samu dan wasan da laifin aikata fyaden, bayan da ya yi rashin nasarar daukaka kara, inda wata kotu a Italiya ta tabbatar masa da hukuncin.
Daga nan ne masu shigar da kara a Italiya suka mika takardun izinin kamo shi daga Brazil.
Robinho wanda ya yi kaka biyu a Manchester City, ya sanar da wani kamfanin dillacin labarai a Brazil cewar da amincewar matar aka yi lalata da ita.
Dan wasan ya dauki kofin La Liga biyu a kaka hudun da ya yi a Real Madrid daga nan ya koma Etihad a matakin wanda aka saya mafi tsada a Burtaniya kan £32.5m.
An kuma sayi dan kwallon a ranar karshe da za a rufe kasuwar cinikin 'yan kwallo a Satumbar 2008 - kuma a karon farko da Sheikh Mansour ya fara aiki a matakin wanda ya mallaki Manchester City.
Bayan kaka biyu da City daga nan ya koma AC Milan, kungiyar da ya yi kaka biyar daga nan ya koma China a kungiyar Guangzhou Evergrande.
Bayan da ya kammala taka leda a China, sai ya koma Brazil a kungiyar Atletico Mineiro.











