An daina amfani da riga mai lamba shida a gasar kwallon Kwando ta Amurka

An wallafa

Hukumar Kwallon Kwando ta Amurka, NBA, za ta karrama marigayi Bill Russell wanda ya dauki kofin gasar sau 11, ta hanyar hana amfani da riga mai lamba shida a dukkanin wasannin gasar.

A watan da ya gabata ne gwarzon dan wasan kwandon na kungiyar Boston Celtics ya rasu yana da shekara 88.

'Yan wasan da suke amfani da riga mai lamba shida a yanzu sun hada da LeBron James, wadanda za su iya ci gaba da amfani da lambar, amma kuma ba za a sake ba wani sabon dan-wasa ba.

Russell ya dauki kofin gasar ta NBA sau 11, da lambar dan-wasa mafi daraja sau biyar a tsawon shekara 13 da ya yi wasa a Celtics.

Haka kuma ya kasance kyaftin din tawagar Amurka a gasar wasannin Olympic ta 1956 inda suka ci lambar zinare, sannan ya yi tasiri sosai a matsayinsa na bakar fata na farko mai horad da 'yan wasa, tare da fafutukar yaki da wariya.

Da wannan mataki yanzu Russell ya kasance dan wasa na farko da hukumar kwallon kwandon Amurka ta hana amfani da riga mai lamba shida, lambar da yake amfani da ita a duk wasannin gasar.

Daman kuma tuni kungiyarsa ta Celtics ta yi hakan.

Baya ga wannan hukumar ta NBA, za ta kuma karrama shi a duk tsawon kakar wasan kwallon kwando ta bana 2022-23, inda 'yan wasa za su rika sanya wani dan kyalle a bangaren dama na kafadar rigar wasansu.

Sannan kuma a duk wani filin wasa na gasar ta Amurka za a yi wani zane da ya hada da lamba shida a gefe, kusa da mai rubutu kwallon da aka ci a wasa.

Shi dai Russell ya samu shiga jerin fitattun gwarazan 'yan wasan gasar na tarihi a 1975, sannan kuma ya sake shiga wannan kundi a matsayin mai horad da 'yan wasa a 2021.

Yanzu ya zama mutum na uku da aka daina amfani da lambar rigar wasansa a manyan gasar wasanni iri daban-daban hudu a Amurka da Kanada

Sauran su ne Jackie Robinson na babbar gasar wasan Baseball, na kungiyar Brooklyn Dodgers mai lamba 42, wanda aka hana amfani da rigar a 1997.

Ita ma riga mai lamba 99 ta gwarzon wasan kwallon gora ta kankara Wayne Gretzky an hana duk kungiyoyin wasan amfani da ita a 2000.