Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Liverpool ta sanar da cin ribar kasuwanci a 2021/22
Liverpool ta sanar da cin ribar fam miliyan 7.5 a kakar 2021/22, inda kungiyar ta ce ta samu karin fam miliyan 107 zuwa fam milyan 594.
A kakar bara kungiyar Anfield ta buga wasa 63 da lashe FA da Carabao Cup da zuwa wasan karshe a Champions League.
Real ce ta ci Liverpool 1-0 a Faransa ta lashe kofin zakarun Turai na 14 jimilla.
Liverpool ta rasa kofin Premier League a bara a ranar karshe da Manchester City ta lashe.
Liverpool ta sanar da cin riba a karon farko tun bayan 2018/19, duk da cewar kudin gudanar da kungiyar ya karu zuwa fam miluyan 69.
Ta samu karin kudin shiga a kallon wasanni daga fam miliyan 83 zuwa fam miliyan 86, bayan da magoya baya suka koma shiga sitadiya, bayan dakile cutar korona
A wannan watan mai Liverpool, John Henry ya ce ba zai sayar da kungiyar ba, amma yana sa ran kara samun hannun jari.
Liverpool ta yi sama zuwa mataki na uku daga na hudu a jadawalin Deloitte, kamfanin kididdiga da kasuwancin tamaula a duniya.
Kungiyar Anfield na biye da Manchester City wadda ta lashe Premier League a bara da mai Champions League, Real Madrid a kididdigar ta Deloitte.
Sai dai Liverpool na fuskantar kalubale a bana, wadda take ta bakwai a teburi, watakila ta kasa samun gurbin Champions League a badi.
Liverpool ta dauki sabbin 'yan wasa har da Luis Diaz kan fam miliyan 37 - yayin da Jordan Henderson da Harvey Elliott da Ibrahima Konate da Andy Robertson da Alisson Becker da Stefan Bajcetic da kuma Diogo Jota duk sun sabunta zamansu a Anfield.