Atletico da Real sun raba maki a wasan hamayya a La Liga

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Atletico da Real Madrid sun tashi 1-1 a wasan mako na takwas a gasar La Liga da suka fafata ranar Lahadi a Metropolitano.

Eder Militao ne ya fara cin ƙwallo, ya zama ɗan Brazil na 17 da ya zura a raga a wasan hamayyar ƙungiyoyin birnin Madrid, kuma na farko tun bayan Rodrygo ranar 18 ga watan Satumbar 2022.

Daf da za a tashi daga karawar Atletico ta farke ta hannun Ángel Correa, kenan sun raba maki a tsakaninsu.

To sai dai Atletico ta karasa fafatawar da ƴan wasa 10 a cikin fili, bayan da aka bai wa Marcos Llorente jan kati.

Da wannan sakamakon Real Madrid ta ci gaba da zama ta biyu a kan teburin La Liga da maki 18 da tazarar maki uku tsakani da Barcelona mai jan ragama.

Atletico tana mataki na ukun teburi da maki 16, bayan nasara huɗu da canjaras uku aka doke ta wasa ɗaya daga karawa bakwai.

Ranar Laraba 2 ga watan Oktoba, Atletico za ta je Benfica, domin buga Champions League, sannan ta ziyarci Real Sociedad a wasan La Liga ranar Lahadi 6 ga watan Oktoba.

Ita kuwa Real Madrid za ta kara da Lille a Champions League a Faransa ranar Laraba 2 ga watan Oktoba, daga nan ta kece raini da Villareal a La Liga ranar Asabar 5 ga watan Oktoba a Santiago Bernabeu..

Wasannin da ak buga tsakanin Atletico da Real a 2023/2024

La Liga Lahadi 4 ga watan Fabrairun 2024

  • Real Madrid 1 - 1 Atl Madrid

Copa del Rey Alhamis 18 ga watan Janairun 2024

  • Atl Madrid 4 - 2 Real Madrid

Spanish Super Cup Laraba 10 ga watan Janairun 2024

  • Real Madrid 5 - 3 Atl Madrid

La Liga Lahadi 24 ga watan Satumban 2023

  • Atl Madrid 3 - 1 Real Madrid

Real Madrid ta buga wasan na hamayya ba tare da Kylian Mbappe ba, wanda yake jinya.