Wasu takardu da aka kwarmata sun ce Amurka ta dakatar da tallafi ga duniya

Asalin hoton, Getty Images
Ma'aikatar harkokin wajen Amurka ta dakatar da kusan dukkannin tallafin da take bai wa ƙasashen waje da take bayarwa tare da tsayar da sabon tallafin da gwamnatin Biden ta shirya bayarwa, kamar yadda wata takarda da aka aikewa jami'ai da ofisoshin jakadancinta a ƙasashen duniya.
Takardar wadda aka kwarmata ta dai na zuwa ne bayan da shugaba Trump ya bayar da umarnin dakatar da dukkan wani tallafi na kwanaki 90 har zuwa lokacin da za a sake yin duba ga tsarin tallafin.
Amurka ce dai ƙasar da ta fi bayar da tallafi a duniya, inda take tallafawa da kuɗin da suka kai dala biliyan 68 a 2023 kamar yadda alƙaluman gwamnati suka nuna. Sabuwar dokar za ta shafi komai kama daga tallafi domin cigaba da tallafin soji ga ƙasashen duniya.
Sai dai kuma dakatarwar ba ta shafi aikewa da taimakon gaggawa na abinci da tallafin soji ga Isra'ila da Misra. BBC ta tabbatar da sahihancin takardun da aka kwaramata
Dave Harden, tsohon darektan hukumar bayar da agaji na Amurka a Gabas ta Tsakiya, ya shaida wa BBC cewa umarnin "na da matuƙar muhimmanci", inda ya ce hakan ka iya dakatar da yawan tallafin kuɗi da kaya da na abinci da Amurka ke bai wa ƙasashen duniya, a daidai lokacin da ake sake duba tsarin.
Ya ce dakatarwar za ta shafi abubuwan cigaba da dama kamar shirin samar da tsaftataccen ruwan sha da muhalli.
Kamfanin dillancin labarai na AFP ya rawaito cewa dakatar da tallafin ka iya shafar ƙasar Ukraine wadda ta karɓi makamai na biliyoyin daloli lokacin Joe Biden.
Sakataren harkokin wajen na Amurka, Marco Rubio ya ce dakatarwar za ta bai wa sabuwar gwamnatin dama yin duba na tsanaki wajen ganin cewa tallafin yana tafiya yadda ya kamata sannan bisa tsarin Donald Trump kan ƙasashen waje.
Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da ake samun ƙarin yawaitar shigar tallafin abinci zuwa Gaza bayan cimma yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin Isra'ila da Hamas da ma sauran ƙasashen duniya da ke fama da yunwa sakamakon rikici kamar Sudan.
Rubio ya ce an bai wa ƙasar Isra'ila da Misra ɗagi dangane da kuɗaɗen da ake buƙata ga sojojin ƙasashen biyu kamar albashi.












