Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
PSG ta kammala ɗaukar Neves daga Benfica
Paris St-Germain ta kammala sayen ɗan wasan Benfica, Joao Neves kan kudi fan miliyan 60.
Ɗan wasan tawagar Portugal, mai shekaru 19, wanda aka yi ta alakanta shi da Manchester United, ya rattaba hannu kan kwantiragin kaka biyar a PSG.
Ya fara buga wa babbar ƙungiyar Benfica tamaula a watan Janairun bara, wanda ya taka rawar gani sosai da yin wasa 75 da cin ƙwallo huɗu.
Neves ya koma PSG, bayan da ƙungiyar mai rike da kofin Ligue 1 za ta fara kakar bana ba tare da Kylian Mbappe ba, wanda ya koma Real Madrid.
Shugaban PSG, Nasser Al-Khelaifi ya ce "Joao yana ɗaya daga cikin hazikan 'yan wasa a Portugal da sauran kasashen duniya."
"Ya kasance mai sha'awar buga wa Paris St-Germain tamuala, kuma ya kuduri aniyar neman gurbin buga wasa a koda yaushe - abin da muke tsammani daga dukkan 'yan wasanmu."
Neves ya buga wa Portugal wasa tara da yin biyu a gasar cin kofin nahiyar Turai a Euro 2024, inda suka kai kwata fainals.