Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
COP 27 : Dalilin da ya sa yarjejeniyoyin da aka cimma kan sauyin yanayi ba su yi tasiri ba
A cikin jerin jawabai da suka yi, shugabannin kasashen duniya sun yi kira ga kasashe masu karfin tattalin arziki da su tsaya tsayin daka wajen daukar matakai domin shawo kan illolin da sauyin yanayi ke haifarwa duk da cewa akwai wasu matsalolin a gabansu da suka hada da yakin Ukraine da kuma na kudi.
Kasashe da ke sahun gaba wajen ganin an dauki mataki a kan sauyin yanayi sun bayyana illar da yanayin zafi da fari da ambaliyar ruwa ke janyowa ga mutane da muhalli.
Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya shaida wa taron cewa, duniya ta kama hanya gadan-gadan za ta shiga bala'in sauyin yanayi.
Shi ma firaministan Birtaniya Rishi Sunak ya bayyana cewa yakin Ukraine shi ne dalilin da ya sa ake bukatar daukar matakin shawo kan sauyin yanayi cikin gaggawa.
Shugaba Emmanuel Macron na Faransa kuwa kira ya yi ga shugabannin duniya a kan bukatar ganin cewa sun yi wa yanayi adalci.
Yayin da Shugaban Gwamnatin Jamus Olaf Scholz yake cewa amfani da makamashin da ba ya gurbata muhali shi ne mafita.
Sai dai kuma a daya bangaren kasashe masu tasowa sun koka ne a kan matsalolin da suke fuskanta sanadin sauyin yanayin.
Firaministar Barbados Mia Mottley ta yi magana ne a kan illar da sauyin yanayi ke janyo wa duniya.
Ta kuma ce har yanzu kasashe masu tasowa ba sa samun tallafin da ya kamata da zai taimaka mu su wajen shawo kan illolin sauyin yanayin.
''Duniyar ta na cikin wani yanayi kamar na zamanin da ke karkashin mulkin mallaka.Kasashen Turai na bayar da rance a kan kashi daya zuwa hudu na kudin ruwa yayin da kasashe masu tasowa na samun rance ne a kan kashi goma sha hudu cikin dari na kudin ruwa, a don a haka ta yaya yarjeniyoyin makamashin da aka cimma za su yi tasiri ? ''in ji ta.
Shi ma Shugaba William Ruto na Kenya ya ce lokaci na kurewa kuma ya kara da cewa ”duk wani jinkiri zai sa mu koma 'yan kallo yayin da aukuwar bala'i za ta janyo asarar rayuka da kuma ta dukiyoyi.
Ya kuma ce mutum miliyan 700 za su rasa matsuguni a nahiyar Afrika saboda rashin ruwan sha nan da shekarar 2030.
A ranar Lahadi ne aka bude taron tare da gargadi daga Majalisar Dinkin Duniya a kan cewa duniya na aike da sako da ke cewa tana cikin fitina.
Wani rahoto da Hukumar kula da Makamashi ta Majalisar Dinkin Duniya ya bayyana cewa shekaru takwas da suka gabata na kan hanyar zama mafiya zafi a tarihi.