Yadda aka wawushe wa ɗan kasuwa kayan ‘sama da miliyan 100‘ a Abuja

An wallafa

A baya-bayan nan ne wasu mutane da ake jin sun kai 300 suka fasa wani rumbun ajiye kayyaki a unguwar Karmo da ke wajen Abuja, babban birnin Najeriya inda suka wawashe shi.

Rumbun, a cewar Murtala Ibrahim, ɗan kasuwa a yankin na Karmo, yana cike da kayan da kuɗinsu ya kai naira miliyan ɗari biyu da goma.

Ya ce bayan wawason da mutanen suka yi, kayan da ya rage bai wuce na naira miliyan cassa'in ba.

Murtala Ibrahim ya kuma bayyana yadda dandazon mutanen suka farfasa motar mutumin da ke da rumbun da ya zo kai ɗauki.

Shi ma Mallam Saleh Zakiru da ke gadin rumbun ya shaida wa BBC cewa mutanen sun dira kan rumbun suna cewa "rumbun na gwamnati ne".

Ya ce wasu sun kwashi kayan ne sun fice daga Abuja zuwa wasu garuruwan.