Ayyukan ƙoda a jikin ɗan'adam da yadda za a gane ta samu matsala

Ayyukan ƙoda a jikin ɗan'adam da yadda za a gane ta samu matsala
An wallafa

Yau ce ranar cutar koda ta duniya wadda hukumar lafiya ta duniya ta kebe domin wayar da kan al’umma dangane da illlolin cutar ta koda.

Albarkacin wannan rana, Dr Mujahid Sunusi, kwararren likitan koda a asibitin koyarwa na Malam AMinu kano, AKTH da ke birnin Kano ya yi karin haske dangane da ayyukan koda a jikin dan adam da kuma yadda mutum zai fahimci lokacin da kodar tasa ta samu matsala.

Alkaluma dai sun nuna cewa akwai masu fama da cutar koda kimanin mutum miliyan 800 a fadin duniya.