Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Michail Antonio ya yi haɗarin mota in ji West Ham
Ɗan wasan West Ham United, Michail Antonio ya yi haɗarin mota in ji ƙungiyar da ke buga Premier League.
A wata sanarwar da West Ham ta fitar ta ce ''Mahukunta da kowa da kowa na yi wa ɗan wasan addu'ar samun sauki tare da iyalai da abokansa a irin wannan lokacin.''
Ƙungiyar ta kara da cewar ''Za ta fitar da karin bayanai nan gaba''.
West Ham za ta kara da Wolverhampton a wasan mako na 15 a Premier League ranar Litinin.
Antonio mai shekara 34 ya koma West Ham daga Nottingham Forest a 2015, kawo yanzu ya ci ƙwallo 68 a wasa 268 a lik da ya buga wa ƙungiyar.
Ƙungiyoyi Premier League da dama sun taya West Ham yin addu'a a kafar sada zumunta ta neman sauki ga Antonio da ya haɗa da Everton da Southampton da Fulham da kuma Brentford.