Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Real Madrid ta fara shirin fuskantar Alaves ranar Talata a La Liga
Real Madrid ta fara shirin karɓar bakuncin Alaves a wasan La Liga mako na bakwai a Santigo Bernabeu.
Ranar Asabar 21 ga watan Satumba, Real Madrid ta doke Espanyol 4-1 a wasan mako na shida, tana ta biyu a teburi da maki 14.
Ƴa wasan Real Madrid sun fara motsa jiki a rufaffen ɗaki bayan nan sai suka fito cikin fili, inda suka dunga raba tamaula da tsalle-tsalle da guje-guje.
Har yanzu Alaba da Ceballos da Camavinga da kuma Brahim na ci gaba da yin atisaye a kokarin da suke na murmurewa.
Real ta doke Alaves gida da waje a bara a La Liga, inda ta je ta fara da cin 1-0 ranar Alhamis 21 ga watan Disambar 2023, sai ta ɗura 5-0 a wasa na biyu ranar Talata 14 ga watan Mayun 2024.
Real Madrid tana mataki na biyu a teburin La Liga da maki 14 a wasa shida, bayan canjaras biyu da lashe karawa huɗu a babbar gasar tamaula ta Sifaniya.
Barcelona, wadda ta yi ta biyu a bara a La Liga, ita ce ta ɗaya a kan teburi da maki 18, sakamakon da ta yi nasara a dukkan wasa shida da fara kakar nan.
Sakamakon La Liga da Real Madrid ta yi da fara kakar nan.
Liga ranar Lahadi 18 ga watan Agusta
- Mallorca 1 - 1 Real Madrid
Liga ranar Lahadi 25 ga watan Agusta
- Real Madrid 3 - 0 Valladolid
Liga ranar Alhamis 29 ga watan Agusta
- Las Palmas 1 - 1 Real Madrid
Liga ranar Lahadi 1 ga watan Satumba
- Real Madrid 2 - 0 Real Betis
Liga Asabar 14 ga watan Satumba
- Sociedad 0 - 2 Real Madrid
Liga Asabar 21 ga watan Satumba
- Real Madrid 4 - 1 Espanyol
Liga Talata 24 ga watan Satumba
- Real Madrid v Alaves
Wasan da Real Madrid za ta kara nan gaba
Liga ranar Lahadi 29 ga watan Satumba
- Atl Madrid da Real Madrid
Champions League ranar Laraba 2 ga watan Oktoba
- Lille v Real Madrid