Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ina nan a Liverpool ko da an sauya sabon mai kungiyar in ji Klopp
Kocin Liverpool Jurgen Klopp ya ce yana nan kan aikin kungiyar ko me zai faru ga wadanda suka mallaketa a yanzu.
Tawagar Fenway Sports Group (FSG) ta ce tana neman sabbin masu zuba jari, sai dai wasu rahotanni na cewa suna son sayer da kungiyar ne baki daya.
Matakin dai ya janyo fargaba da ce-ce-ku-ce tsakanin magoya bayan Liverpool inda ake tsoron rikici a Anfield, kuma hakan ya janzo tambaya kan makomar kocinta Klopp.
A ranar Laraba, Liverpool ta doke Derby County a bugun fenareti a wasan Carabao.
Da yake bayani karon farko tun bayan fara batun FSG a ranar Litinin, Klopp ya ce ba inda zai je labarin bai sauya shirinsa ba na karawar da za su yi da kungiyar League One.
"Abin da na karanta shi ne suna neman sabbin masu zuba jari," tunani ne mai kyau, ni ma na goyi baya.
"Amma hakan bai bata shirinmu ba ko kadan. Yan wasan ba su ce min komai ba, a wajena hakan baya nufin komai.
"Ina da akala mai kyau da FSG. Ina son yadda suke aiki idan kuma sun sauya, ina nan a kungiyar kuma hakan ba zai shafi mutanen da ke nan ba."
Klopp yace bai kamata a rika kwatanta su da Chelsea ba, wadda ta sauya mamallakinta kuma hakan ya kai ga korar kocin lokacin Thomas Tuchel.