Abin da kuke son sani kan wasan Faransa da Morocco

World Cup 2022

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Za a buga wasan daf da karshe a Gasar Kofin Duniya da Qatar ke karbar bakunci tsakanin Faransa da Morocco ranar Laraba a filin wasa na Khalifa.

Faransa ce mai rike da kofin duniya, wadda ta lashe a Rasha a 2018 na biyu jumulla, bayan wanda ta dauka a 1998 da ta karbi bakuncin wasannin.

Wannan shi ne karon farko da Morocco za ta buga daf da karshe a Kofin Duniya ta daya a Afirka da ta yi wannan namijin kwazon tun lokacin da Fifa ta fara wasannin daga 1930.

Sai dai kasashen Afirka uku sun taba kai wa zagayen daf da na kusa da na karshe a babbar Gasar tamaula ta duniya da ya hada da Ghana da Senegal da Kamaru sai Morocco da ta kai har matakin daf da karshe.

Faransa ta kawo wannan matakin, bayan nasara a kan Ingila da ci 2-1 a wasan daf da na kusa da na karshe ranar Asabar.

A kuma ranar Morocco ta fitar da Portugal, bayan nasara da ci 1-0, kuma Youseff En-Nesyri ne ya ci kwallon saura minti uku su je hutu.

Wannan shi ne wasa na biyar da za su kara a tsakaninsu na farko a Gasar Kofin Duniya, sauran sun hadu ne a wasannin sada zumunta.

Faransa ce ta yi nasara a fafatawa biyu da canjaras biyu a haduwa hudun da suka yi a baya.

Wasan da aka kara tsakanin Faransa da Morocco

Wasan sada zumunta Juma'a 16 ga watan Nuwambar 2007       

France           2 - 2    Morocco      

Wasan sada zumunta Juma'a Talata 6 ga watan Yunin 2000       

Morocco       1 - 5    France          

Wasan sada zumunta Juma'a Laraba 20 ga watan Janairun 1999      

France           1 - 0    Morocco      

Wasan sada zumunta Juma'a Juma'a 29 ga watan Mayun 1998      

Morocco       2 - 2    France

Qatar World Cup

Asalin hoton, BBC Sport

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Wasu karin bayanai kan wasan Faransa da Morocco

Da kyar idan dan wasan Faransa mai tsaron baya Dayot Upamecano da mai wasa daga tsakiya Adrien Rabiot za su buga fafatawar, bayan da suka yi atisaye dan kadan ranar Talata.

Upamecano, wanda ke fama da ciwon makogwaro, watakila a maye gurbinsa da Ibrahima Konate.

Walid Cheddira ba zai yi wa Morocco wasan ba, sakamakon jan kati da aka yi masa a fafatawa da Portugal.

Sai dai kuma da kyar idan Nayef Aguerd zai buga karawar, wanda bai yi wasa da Portugal ba, saboda da jinya.

Haka shima Romain Saiss da kyar idan zai iya buga gumurzun, wanda ya ji rauni a fafatawa da Portugal.

Tun farko Noussair Mazraoui bai buga wasa da Portugal ba, saboda rashin lafiya, amma wata kila ya shiga wasa da Faransa ranar Laraba.

Wasu batutuwan da ya kamata ku sani kan wasan

An fitar da Faransa daga wasa uku a daf da karshe a baya a 1958 da 1982 da kuma 1986 daga nan ta lashe uku da ta buga a gaba a 1998 da 2006 da kuma 2018.

An zura kwallo a ragar Faransa a wasannin da ake yi a Qatar kuma sau 11 tun daga watan Yuni.

Morocco ce kasa ta 25 da za ta buga daf da karshe a Gasar Kofin Duniya, kuma ta farko a Afirka da ta yi wannan namijin kokarin.

Tawagar da ta taba kai wa wannan matakin a karonta na farko har ta lashe Kofin Duniya ita ce Sifaniya, wadda ta ci Jamus 1-0 a wasan karshe a 2010.

Morocco ta yi wasa hudu kwallo bai shiga ragarta ba a wasannin da ake yi a Qatar.

Tawagar da ta buga fenaritin raba gardama biyar a Gasar Kofin Duniya a sekarar da ake yi wasanin ita ce Sifaniya a 2010 da kuma Italiya a 2006.