Qatar na son Fifa ta hana giya a Kofin Duniya, Argentina ta tafi gasar da tarin nama

Asalin hoton, Getty Images
Tawagar Argentina da ta Uruguay da suka tafi gasar Kofin Duniya sun yi dakon tarin nama mai yawa zuwa Qatar domin su rika tunawa da dandanon abincin kasashensu a lokacin gasar.
‘Yan kasar Qatar na son hukumar kwallon kafa ta duniya, Fifa ta sauya shawarar da ta yanke ta barin a sayar da barasa a dukkanin filayen wasannin da za a yi gasar Kofin Duniya.
Watakila cinikin matashin dan wasan tsakiya Jude Bellingham na Ingila mai shekara 19 da Liverpool ya kammala, inda ake sa ran ya bar Borussia Dortmund.
Tsohon dan gaban Liverpool Emile Heskey ya ce kungiyar ta Anfield ta tashi tsaye sosai har sai ta ga ta samu matashin dan wasa.
Haka kuma Liverpool din da Juventus na jira su ga yadda za ta kaya a tattaunawar yarjejeniyar da ke wakana tsakanin dan wasan tsakiya na Ingila Mason Mount da Chelsea.

Asalin hoton, Getty Images
Chelsea na kallon Mount a matsayin wanda zai iya zama kyaftin din kungiyar a nan gaba, amma kuma kwantiragin matashin dan wasan na yanzu ya sa ya zama daya daga cikin wadanda ke karbar albashi mafi karanci a kungiyar.
Tsohon kocin Tottenham da Southampton da kuma Paris St-Germain Mauricio Pochettino ya ce a shirye yake ga duk wani tayi, lokacin da aka tambaye shi ko yana da sha’awar zama kocin tawagar Ingila.
Fulham da Bayer Leverkusen da kuma Villarreal na sha’awar sayen dan bayan Portugal Cedric Soares, daga Arsenal a watan Janairu.
Aston Villa ta yi watsi da damarta ta sayen dan wasan tsakiya na Portugal Joao Palhinha kafin dan wasan mai shekara 27 ya tafi Fulham.
Tsohon dan gaban Barcelona da Liverpool Luis Suarez, mai shekara 35,ya yi watsi da tayin zuwa kungiyar Gremio ta Brazil idan kwantiraginsa da Nacional ta kasarsa Uruguay ya kare.
Jiragen yaki sun yi wa tawagar kwallon kafa ta kasar Poland da za ta je gasar Kofin Duniya rakiya zuwa Qatar.










