Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Burin mata na zama limaman coci ya fara cika
Anne Tropeano na goge tufafin da za ta sanya, domin tanadin yadda ranar za ta kasance gare ta. Ta ɗaga doguwar farar rigarta, da wani maɗauri na musamman da malaman coci ke amfani da shi a sassan duniya.
Ta duba kalandar da ke saƙale a bango, ta yi rubutu ɓaro-ɓaro a jikin kwanan watan da abin rubutu launin ja, ya nuna gobe ''ranar karɓuwa ce.''
Tana kuma riƙe da wayar tarho don hayar ƙarin jami'an tsaro da za a baza a ciki da harabar cocin da ke Albuquerque, a jihar New Mexico, inda take zaune, saboda ko-ta-kwana idan an ta da hatsaniya.
"Batu ne da ya janyo ce-ce-ku-ce, ba kowa ne ke na'am da wayar gari a kira mace matsayin limamiyar coci ba.'' Ita fa Tropeano ba komai take tsoro ko gujewa ba, sai tashin hankali.
Tun lokacin da ta fara bayyana muradinta na zama malamar coci, take fama da matsaloli ciki har da na cin zarafi a shafin intanet.
Tropeano ɗaya ce a cikin sama da mata 250 a duniya da ke neman zama wani ɓangare na jagorancin cocin Roman Katolika, wasu dai na kallon hakan tamkar wani yunƙuri ne na fito na fito da limamai maza.
Cocin Katolika ba ta amince da limamai mata ba. Hasali ma, Batikan na kallon hakan a matsayin babban zunubi, da aka tanadi tsattsauran hukuncin a kai.
Hakan na nufin da zarar an zo tantance shi ke nan ba sa iya zuwa komai ciki har da jana'iza.
Wasu dai na ganin kama daga Yahudawa har zuwa sauran addinai bai dace mata su yi limanci ba. Amma duk da haka, matsayin Cocin Katolika na haramta wa mata zama limamai ya sha banban da na sauran, misali idan mace ta daɗe a kan layin tun tana 'yar ƙarama.
Sai kuma wani batun da suke yi shi ne a littafi mai tsarki na Bayibul, Yesu Almasihu ya zaɓi duk mataimakansa 12 daga jinsin maza, bai ɗauki mace ko ɗaya ba, kuma tun daga wancan lokacin cocin katolika ke koyi da abin da Yesu ya shimfida.
Amma ga Tropeano, lamarin ya wuce haka.
"Bisa tarbiyar koyarwar Coci, da ayyukan da take gabatarwa ana nuna muhimmancin mata. Mata na koyar wannan, haka yara, don haka duk inda mace ta shiga tana da wata ɗaukaka."
Shagalin biki a jirgin ruwa
A shekarar 2002 ne aka fara gangamin ganin mata sun shiga sahun limaman coci. Wata ƙungiya mai ɗauke da mata bakwai, sun shiga gangamin hakan cikin jirgin ruwa a kogin Danube, don kauce wa rikicin addini.
Duk da haka, akwai rahotannin da suka bankaɗo wasu sirrika na baya game da naɗin mata, misali kamar Ludmila Javarova an naɗa ta limamiyar cocin Czechoslovakia a shekarun 1970, ta kuma shiga rukunin bishop-bishop na cocin Katolika.
Gangamin da mata ke yi na ganin an dama da su a cocin Roman Katolika an fi yi ne a ƙasashen Turai da Amurka, duk da yake an fara ganin tasirin yaɗuwar sa a sauran ƙasashe.
Mace ta farko da ta rike irin wannan muƙami, ita ce Olga Lucía Álvarez Benjumea ta Colombia, ita ce mace ta farko da aka naɗa Limamiyar Cocin Katolika, mai mabiya sama da miliyan 1.3 sassan duniya.
Bikin nadinta a shekarar 2010, an yi shi ne a asirce, amma ta ce ta samu gudunmawar ƙananan majami'u; "Cikin waɗanda suka zo akwai wani bishop na ɗarikar katolika, wanda ba zan bayyana sunansa ba saboda dalilan tsaro…."
"A tsorace nake, saboda mutane za su fara min wulaƙanci da rashin mutunci, wataƙil har da jifa na idan ina wucewa a cikin coci, musamman a wannan sabuwar duniyar ta masu tsaurin ra'ayin addini.
"Amma irin goyon bayan da mutane suka nuna min ba zai misaltu ba, sun ba ni ƙwarin gwiwa, kuma sun tsaya min a lokacin," in ji Álvarez. A yanzu an ƙara mata girma zuwa bishop ta Roman Katolika kuma a yanzu Batikan ta amince da ita.
Álvarez ta fito daga gidan addini sosai na Katolika, ta kuma samu goyon bayan dan'uwanta limamin coci, yayin da mahaifiyarta ta kasance mi hidima ga cocin. Dan'uwanta ya ba ta kyautar da take kallo a matsayin toshiyar baki.
Álvarez ta kafe cewa babu a inda Littafi Mai Tsarki ya ware mace, da haramta mata wasu muƙamai ko kai wa wani matsayi.
Babbar darakta Kate McElwee, ta ce bin da ya fi ba ta sha'awa a aikin da take yi shi ne kasancewa a wani sashen ba da agaji da taimako, inda take ganin tarin masoya da masu goyon baya.
Ana sakin hayaƙi launin ruwan hoda da ke fara fita kafin jerin gwanon motocin Paparoma su taho a duk lokacin da zai zagaya gari. 'Yan sanda sun taɓa kama su lokacin da suka yi shigen hakan tare da tsare su tsawon kwanaki.
"Muna tafe da matan, lokacin da suke cikin hutu, sun tsaya jiran a buɗe ƙofar Fadar Batikan, don su ƙalubalance su da laifukan d suke aikatawa na baɗala," in ji McElwee. "Amma ga wasu matan ba za su taɓa yi ba, saboda tsoro, yadda muke ƙwalla ihu da kiran sunan Allah, ba su da zaɓi face su buɗe mana ƙofa."
An rufe kofa
Bayan an yaɗa labarin abin da ya faru, sai babban malamin coci Cardinal Joseph Ratzinger, wanda daga bisani ya zama Fafaroma Benedict, ya ayyana cewa tun da matan ba su nuna wata alama ta karaya ko nadama ba, kan laifukan da suka aikata, to an zartar da za su fuskanci hukunci.
Fafaroma Francis da kansa ne ya zartar da hukuncin naɗa mace ta farko a matsayin limamiya. A shekarar 2016, da aka tambaye shi ko akwai yiwuwar wani sauyi, ya ba da misali da shekarar 1994 a zamanin Fafaroma John Paul II kan cewa "an rufe ƙofar" barin mata su yi shugabanci irin wannan, kuma Fafaroma ya tabbatar da haka.
Malama Nathalie Becquart, ta yi aiki a ofishin Fadar Batikan, tana da hoton da aka ɗauke su tare da Fafaroma Francis tana tsaye a bayan shi. A watan Fabrairu 2021, ita ce mace ta farko da ta riƙe matsayin mataimakiyar sakataren ba da shawara ga Fafaroma. Ta bayyana halin da mata limaman coci ke ciki a halin yanzu da cewa akwai abin damuwa, amma ta zaɓi yin shiru ne saboda muƙamin da take riƙe da shi.
"Ina ganin ya dace mu faɗaɗa tunani da hangenmu kan ainihin koyarwar cocin. Akwai hanyoyi da dama da mata za su iya aiki da hidima a coci, Ba tare da an yi fito na fito ba," in ji Becquart.
Amma kuma ta amince ba lamari ne mai sauƙi ba, kawo irin wannan sauyi a lokaci guda, a ko da yaushe fargaba da tsoro kan ɗarsu a zukatan mutane.
Me Fadar Batican ke cewa?
•Bisa ɗabi'a ta Cocin Katolika, abin da suka yi haramtacce ne kuma ya saɓa wa doka. sun kare matakin da cewa namiji ɗaya da aka yi wa wankan Baftisma, yana kasancewa a tafarkin dokokin kotun katolika. (Canon 1024).
•A shekarar 2021 an yi wa dokokin Cocin Katolika kwaskwarima, Duka dai kan batun bai wa mata jagoranci. Babu wani wuri da ya nuna ɗaukar mataki a kai.
•A baya-bayan nan Fafaroma Francis ya nuna alamun buɗe wata kafa da za a samu matan to amma akwai abubuwan da ba za su iya yi ba. Cikin abin da za su yi an amince su halarci ɗaurin aure a matsayin shaidu, da kuma jana'iza.
•A wani mataki na bazata, Fafaroman dai ya buƙaci jin ra’ayi mabiya ɗariƙar, kan yadda suke kallon lamarin da kuma makomar Cocin nan gaba. Za a yi ta jin bahasin jama’a daga nan har zuwa shekaru biyu masu zuwa.
•Wani bincike da aka gudanar ya nuna rawar da mata ke takawa a Cocin, ana kuma sa ran tattauna kan haka a Babban taron da za a yi cikin watan Oktoban baɗi.
•'Yar uwa Nathalie Becquart ta shaida wa shirin BBC na fitattun mata 100, cewa bayan nan ne Fafaroma zai san matsaya ko matakin da za a ɗauka.
Hanyoyi daban-daban
Anne Tropeano ta tunkari duk wanda aka san ya ba da matsayin malami a coci, ciki har da bishop ɗin ta, kuma ta tabbatar masa cewa ta shirya.
Rana ce da ta daɗe tana jira tsawon shekara 14. Ranar da za ta zama malamar coci kamar sauran da suka daɗe suna addu’o’i.
A lokacin taron, bishop ɗin ya ce ya sassauta wa Anne Tropeano ne don yi wa sauran jagora. Tare da gabatar da ita a matsayin sabuwar limamiya.
Tropeano ta ce farin ciki ya baibaye zaciyarta, Kasancewar ta sabuwar fuska a cocin . Lamarin da ba kasafai ake gani ba.