Reece James na bukatar ganin kwararru kan raunin gwiwarsa

An wallafa

Reece James zai ga kwararru likitocin gywaran gwiwa - bayan raunin da ya ji a gasar Champions a ranar Talata, in ji kocin Chelsea Graham Potter. An cire dan bayan da yake buga bangaren dama a minti na 62 da fara wasan, wanda Chelsea ta yi nasara a kan AC Milan - bayan raunin da ya ji wajen kokarin kwace kwallo. Potter ya yi gargadin cewa a bi a hankali, lokacin da ake nuna damuwa game da cewa dan wasan Ingilan zai iya gaza buga gasar cin kofin duniya. "Babu dalilin da za a rika hasashen kan abun da bai zoba tukunna," in ji shi. "Muna bukatar mu duba kan mu yanke hukunci." Ya ce: "Reece zai ga kwararrun likitoci a karshen mako to babu abin da za mu iya yi har sai mun samu bayani daga gare su, babu wani abu da zan iya yi. "Saimun duba nutsuwarsa da kuma ganin kwararru. A jiya ya dan samu sauki amma ba za mu iya komai ba sai mun samu bayanan likitoci."