Arsenal ta koma ta biyu a Premier bayan nasara a kan Liverpool

Premier

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Arsenal ta koma ta biyu a teburin Premier League, bayan da ta doke Liverpool 3-1 a wasan mako na 23 a Emirates ranar Lahadi.

Gunners ta fara cin kwallo a minti na 14 da fara wasa ta hannun Bukayo Saka, daga baya Liverpool ta farke bayan da Gunners ta ci gida ta hannun Gabriel Magalhaes.

Bayan da wasa ya nutsa a zagaye na biyu ne Arsenal ta kara na biyu ta hannun Gabriel Martinelli.

Liverpool ta rasa ɗan wasa daya, bayan da aka bai wa Ibrahima Konate jan kati, sai dai daf da za a tashi Gunners ta kara na uku ta hannun Leandro Trossard.

Da wannan sakamakon Arsenal ta koma ta biyun teburi da maki 49 da tazarar maki biyu tsakaninta da Liverpool ta daya.

Arsenal ta buga karawar ba tare da Gabriel Jesus, wanda ke jinyar raunin gwiwa.

An kuma ajiye Jesus da Emile Smith Rowe, wadanda sun buga wasan da Arsenal ta ci Nottingham Forest a tsakiyar mako, yayin da Jorginho da Kai Havertz suka maye gurbinsu.

Liverpool kuwa sauyi uku ta yi daga ƴan wasan da suka doke Chelsea a gasar Premier League a tsakiyar mako.

Conor Bradley, wanda mahaifinsa ya mutu, bai samu zuwa fafatawar ba, bayan da Dominik Szoboszlai ke jinya, Darwin Nunez na benci.

An fara wasa da Trent Alexander-Arnold da Cody Gakpo da kuma Ryan Gravenberch.