Manyan matsaloli takwas da ke addabar ƴan Afirka ta Kudu gabanin zaɓe

Asalin hoton, AFP
- Marubuci, Damian Zane, Dorothy Otieno & Olaniyi Adebimpe
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News
- An wallafa
Afirka ta Kudu, ɗaya daga cikin ƙasashe mafiya arziki da tasiri a Afirka, na shirin kaɗa ƙuri'a a zaɓuka na ranar 29 ga watan Mayu yayin da ake fargaba game da rashin aikin yi, da ƙaruwar laifuka, da kuma ɗaukewar lantarki.
A waɗannan tasawirorin, za a ga manyan abubuwan da za su mamaye wannan zaɓe - karo na bakwai ke nan tun bayan fara zangon dimokuraɗiyya a 1994.

Idan ƙuri'ar jin ra'ayin jama'a da aka gudanar ta yi daidai, to lallai za a shiga sabon mataki a fagen siyasar ƙasar.
Jam'iyyar African National Congress (ANC) mai mulki ce ta mamaye fagen siyasar ƙasar tun daga gwagwarmayar da ta yi wajen korar gwamnatin wariya ta fararen fata.
Ta cinye zaɓen farko a 1994 kuma tun daga lokacin take kan mulki.
Amma ƙuri'un da take samua zaɓuka na ci gaba da raguwa tsawon shekaru tun daga 2004, lokacin da ta samu mafi yawan ƙuri'u na kashi 70 cikin 100.
Bincike na nuna cewa za ta iya ƙara raguwa zuwa kashi 50 cikin 100, abin da zai sa ta koma yin haɗin gwiwa.

Ɗaya daga cikin abubuwan da ke jawo wa ANC baƙin jini shi ne halin da tattalin arzikin ƙasar ya shiga.
Idan aka duba shekara 30 da suka wuce, 'yan Afirka ta Kudu sun ƙara arziki. Talauci ya ragu, kuma mutane sun samu damar samun gidaje da kuma kiwon lafiya a dunƙule.
Sai dai kuma, an samu raguwar samun kuɗaɗe a adadi na tsakatsaki daga 2011, abin da ya sa wasu da dama kan ji cewa sun ci baya kuma suka fara zargin ANC da yin almubazzaranci da tattalin arzikin ƙasar.

Duba adadi na tsakatsaki kawai ba zai ba da cikakken labarin ƙasar ba, saboda akwai bambancin samu tsakanin al'ummomin ƙasar.
Idan aka yi amfani da tsarin da ake kira Gini coefficient, wanda ke duba yawan abin da kowane iyali daga kowane rukuni na al'umma ke samu, za a ga Afirka ta Kudu ce ƙasa mafi rashin daidaito a duniya.
Misali, kashi 20 na al'ummar ƙasar da suka fi arziki su ne ke riƙe da kusan kashi 70 cikin 100 kuɗaɗen da iyalai ke samu. Idan aka kwatanta, sauran kashi 40 mafiya talauci na riƙe ne da kashi 7 cikin 100 kacal na arzikin ƙasar.

Ɗaya daga cikin manyan abubuwan da ke jawo rashin daidaiton da kuma babbar alamar tasirin taɓarɓarewar tattalin arziki shi ne rashin ayyukan yi, wanda Bankin Duniya ya ce ƙasar ta zarta saura a faɗin duniya.
Tattalin arzikin ba shi haɓakar da zai iya ɗaukar nauyin yawan mutanen da ke neman aiki.

Rashin aikin yi ya fi dabaibaye matasa sosai. Sama da kashi 44 na 'yan shekara 15 zuwa 34 ba su zuwa makaranta, ko horon sana'a, ko kuma ba su da aikin yi.
Kamar wasu ƙasashen Afirka da dama, Afirka ta Kudu na da matasa da yawa - mafi yawan jama'arta miliyan 62 'yan ƙasa da shekara 35 ne.
Wani rahoton Majalisar Ɗinkin Duniya ya siffanta ƙarancin aikin yi a matsayin "wani bam da ke jiran ya fashe", yana mai nuni da cewa hakan ka iya zama dalili na rikicin siyasa.

Jam'iyyun siyasa na alƙawarin kawo ƙarshen aikata manyan laifuka da suka yi wa ƙasar katutu tsawon shekaru.
Alƙaluma sun nuna cewa duk da an samu raguwa kaɗan a adadin aikata laifuka cikin shekara 10 da suka wuce, yawan aikata fashi, da fyaɗe, da kisan kai kamar ba su wani sauya ba.
A lissafi na tsakatsaki, cikin wata uku na ƙarshen 2023, akan kashe mutum ɗaya a Afirka ta Kudu duk minti 20. A dai wannan lokaci, akan yi wa sama da mutum 130 fyaɗe duk a kullum.
Shugaba Cyril Ramaphosa ya siffanta ƙaruwar aikata laifukan a matsayin yaƙi a kan mata, amma ana yawan sukar jam'iyyarsa kan yadda take tunkarar matsalar.

Yanzu haka 'yan Afirka ta Kudu na samun sauƙi daga yawan ɗauke-ɗauken wutar lantarki da aka dinga yi a 'yan shekarun da suka gabata.
Ɗaukewar da aka tsara don rarraba ta tsakanin yankuna, ta jawo ƙunci a rayuwar mutane da kuma daƙile haɓakar tattalin arziki.

Kusan kashi 3 na al'ummar ƙasar, waɗanda suka kai kusan miliyan 2.4, 'yancirani ne da suka shiga Afirka ta Kudu.
Duk da matsin tattalin arziki a ƙasar, har yanzu mutane daga sauran ƙasashe kan je neman arziki.
Amma kuma ana yawan zargin 'yan ƙasar wajen da kankane ayyuka da kuma tunzura ƙaruwar laifuka a ƙasar duk da cewa su ne marasa rinjaye a ƙasar. Hakan ta sa aka dinga kai wa baƙi hari tare da ƙona harkokin kasuwancinsu.
A farkon watannan, ƙungiyar kare haƙƙi ta Human Rights Watch ta ce ana ɗaukar 'yan ƙasar waje a matsayin 'yanbora da kuma ɓata musu suna yayin yaƙin neman zaɓe, abin da ke ƙara ta'azzara kai musu hare-hare.












