Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Zaben Najeriya na 2023: Kola Abiola ya ce ya tsaya takarar shugaban ƙasa ne don ya ci zaɓen
Danna hoton da ke sama don kallon bidiyon...
Dan takarar shugabancin Najeriya a jam'yyar PRP Kola Abiola ya fada wa BBC ya tsaya takara ne don ya ci zabe a shekarar 2023.
Kola dan marigayi Moshood Abiola ne wanda ake cewa shi ya lashe zaben da aka gudanar a shekarar 1993.
Ya ce ya zabi ya tsaya takara a jam'iyyar PRP ce saboda kyawawan manufofi da kuma ginshikanta na siyasa.
A cewarsa, jam'iyyar itace tafi ko wacce dadewa a Najeriya saboda ta faro ne daga NEPU zuwa PRP.
Kola Abiola ya ce idan ya samu nasara zai mayar da hankali kan "ilimi da tsaro da noma da kiwo da kuma samar da ababen more rayuwa ga 'yan Najeriya".
Ya kara da cewa tun ba yau aka kafa manufofin jam'iyyar PRP, kuma manufofi ne masu matukar kyau ga al'umma.