Rikcin Falasɗinawa: Mahara sun kashe mutum 3 da gatari a Isra'ila

Asalin hoton, Reuters
An wallafa
Mutane uku ne suka mutu wasu kuma suka jikkata sakamakon wani hari da aka kai birnin Elad da ke tsakiyar kasar Isra'ila.
Kafofin yada labaran kasar sun ruwaito cewa wasu mahara biyu dauke da wukake, da gatari ne suka auka wa masu wucewa a wani wurin shakatawa.
'Yan sanda na ci gaba da neman wadanda ake zargi, bayan kafa shingayen binciken ababan hawa.
Harin dai ya zo ne a ranar 'yancin kai ta Isra'ila, ranar da jama'a ke hutu a fadin kasar.
Galibin mazauna birnin Yahudawan ne masu tsattsauran ra'ayi.
Kwanan nan dai rikici na karuwa tsakanin Isra'ila da Falasɗinawa musamman lokacin watan azumin Ramadana, lamarin da ya kai ga mutuwar mutane daga dukkan bangarorin biyu.







