DMO: Najeriya ba ta taba jinginar da kadararta ba don karbo bashi

Asalin hoton, MIN OF FINANCE
Ofishin da ke kula da lamuni na Najeriya wato Debt Management Office ya ce Najeriya ba ta taba ba, kuma ba za ta taba jinginar da kadararta da sunan karbar bashi daga China ko wata kasa ba.
A hira da manema labarai ranar Asabar a Abuja, Darakta Janar ta ofishin Ms Patience Oniha, ta yi bayani dalla-dalla cewa basussukan da Najeriya ta karbo daga China babu batun jinginar da kadara a yarjejeniyar da aka kulla kafin karbarsu.
A yanzu bashin da China ke bin Najeriya ya kai dala biliyan 3.59, wanda ya yi daidai da kashi 9.4 na dala biliyan 37.9 da kasashen duniya ke bin kasar.
Kwanan baya ne wasu jaridun cikin gida suka ruwaito cewa kasashen Afrika da dama ciki har da Najeriya na fuskantar barazanar rasa kadarorinsu, matsawar suka gaza biyan China bashin da ta ke bin su.
"Daga ranar 30 ga watan Satumba bashin da ake bin Najeriya ya kai dala biliyan 37.9. Wannan bashi ya kunshi wanda ake bin gwamnatin tarayya. da gwamnatocin jihohi 36 da kuma birnin tarayya," a cewar Ms Patience.
To amma ta jaddada cewa Najeriya ba ta taba kulla yarjejeniyar karbar bashin China da sunan ba da jinginar wata kadara ba inda tace " duk basukan da China ke bam u babu batun jinginar da wata kadara a cikin sharudan karbar sa," in ji ta.
Ta kara da cewa "duk wani bashi da Najeriya za ta karba sai da amincewar ma'aikatar shari'a, wanda hakan abun ne mai muhimmanci."
"Kuma ba haka kawai ake fara batun daukar wasu matakai masu tsauri ba don kawai an gaza biyan bashi. Kasashe na bin hanyoyin warware matsaloli a tsakaninsu ne, sai idan hakan ta gagara sai a tafi kotu."
Babbar daraktar ta ce ofishin nata na kokarin ajiye bayanai d akuma ba da shawarwarin da suka dace kafin karbo bashi daga waje.
Kazalika ta ce DMO na hasashen hanyoyin da za a bi wurin biyan bashin kafin ma a ciyo shi.
A cikin watan Nuwamba aka rika yada cewa China na shirin kwace filin jirgin Uganda saboda gaza biyanta bashin da take bin kasar.
Amma kuma daga bayan gwamnatin China ta fito ta karyata jita-jitar.
Hakan ya sa wasu 'yan Najeriya suka rika tafka muhawara a shafukan sada zumunta kan yadda gwamnatin Najeriya ke karbo basussuka daga waje, suna guje mata cewa za ta iya rasa wata kadara idan har biyan bashin ya buwaya a nan gaba.










