Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
'Yan Najeriya na baya-baya da rigakafin korona- NCDC
Darakta Janar na cibiyar da ke kula da cutuka masu yaduwa a Najeriya,NCDC, Dr Ifedayo Adetifa, ya ce cibiyoyin da ake yin allurar rigakafin cutar korona a kasar na fama da karancin masu zuwa a yi musu rigakafin.
A hira da manema labarai a Abuja, Dr Adetifa ya ce rashin zuwan da ba a yi domin yin allurar, na janyo koma-baya ga kokarin da gwamnati ke yi na magance yaduwar cutar.
Shugaban ya kara da cewa, "ba wai rashin zuwan jama'a a yi musu rigakafin ne kawai matsalar ba, hatta dokokin kare-kai daga kamuwa da cutar ta korona an yi watsi da su."
Ya kara da cewa, "yanzu haka akwai allurar rigakafin koronar da za ta isa a yi wa kashi 50 cikin 100 na wadanda suka cancanci a yi musu rigakafin, amma mutane ba sa son zuwa a yi musu. In ji Dr Adefita.
Kawo yanzu NCDC ta tabbatar da cewa mutum uku sun kamu da sabon nau'in cutar korona na omicron da ya bulla kwanan-nan a Afrika ta kudu.
Kuma yanzu haka dokar hana shiga ma'aikatun gwamnati ga ma'aikatan Najeriya da ba a yi wa rigakafin koronar ba ta fara aiki.
Wasu ma'aikatan gwamnatin sun tabbatar wa da BBC cewa an hana su shiga wuraren aikinsu, saboda kasa gabatar da shaidar da ke nuna cewa an yi musu rigakafin korona, ko kuma gwajin da bai jima ba da ya nuna cewa ba sa dauke da cutar.
NCDC ta kuma ce ana ci gaba da farautar wadanda suka yi mu'amala da mutanen da suka kamu da sabon nau'in.
A watan da ya gabata ne aka bayyana ɓullar sabon nau'in cutar na Omicron a kasar Afrika ta Kudu, abin da ya sa wasu kasashe irin su Birtaniya da Amurka ɗaukar matakin hana tafiye-tafiye zuwa kasashen da ke kudancin Afrika.
Kazalika Hukumar Lafiya ta Duniya wato WHO, ta ɗora alhakin ɓullar sabon nau'in cutar a kan rashin dadaito wajen rarraba alluran rigakafi a tsakanin kasashe.
Ta kuma yi gargadin cewa sabon nau'in cutar zai iya shafe tsawon lokaci yana mummunar barazana ga kasashen duniya.