Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Kasuwar ƴan ƙwallo: Neman sabon kocin United, Madrid kuwa na son Mount, Everton na fatan samun Gray
Kocin Paris St-Germain dan kasar Argentina Mauricio Pochettino ne zabi na daya ga kungiyar Manchester United da ke zummar ganin ya zama kocinta a kakar wasa mai zuwa. An ce babban kocin Ajax, dan kasar Holland Erik ten Hag, shi ne zabi na biyu. (Sky Sports)
Bayanai sun ce shima Pochettino din a shirye yake ya koma kungiyar a bazara mai zuwa. (Telegraph)
Ten Hag ya mayar da martani kan rade-radin cewa zai maye gurbin Ole Gunnar Solskjaer a Manchester United inda ya ce bai ji komai ba game da rade-radin. (Manchester Evening News)
Wakilin 'yan wasan nan na Portugal Jorge Mendes yana ta kokarin ganin Manchester United ta maye gurbin Ole Gunnar Solskjaer da kocin Sevilla Julen Lopetegui.
Dan kasar Sipaniyan da sauran kwantiragi da Sevilla har zuwa shekarar 2024 amma Mendes mai wakiltar Cristiano Ronaldo yana son ganin ya koma Old Trafford. (Manchester Evening News)
Real Madrid na zawarcin dan wasan tsakiya na Chelsea da Ingila Mason Mount. Dan wasan mai shekaru 22 yana tattaunawa da kulob din kan sabon kwantaragi, kodayake an ce "ba ya jin dadin zamansa a kungiyar'' kuma yana iya shirin barin kulob din. Manchester City da Bayern Munich suna zawarcinsa. (Fichajes - in Spanish)
Babban kocin Spain Luis Enrique ya musanta jita-jitar da ake yadawa ta alakanta shi da Manchester United. (Goal)
Sabon kocin Aston Villa Steven Gerrard na son dauko dan wasan bayan Croatia Borna Barisic, mai shekara 29, daga tsohon kulob din da ya murza leda wato Rangers. (Rikodin Kullum)
Kocin Everton Rafael Benitez ya ce kulob din zai nemi sayen 'yan wasa a watan Janairu yayin da dan wasan Ingila Demarai Gray, mai shekara 25, ya zama na baya bayan nan a jerin 'yan wasansu da suka samu rauni yayin karawa da Manchester City. (Liverpool Ec
Dan wasan gaba na PSG Lionel Messi, mai shekara 34, ba ya shirin komawa Barcelona duk da kalaman shugaban kungiyar na cewa za su iya sake daukar kyaftin din Argentina a nan gaba. (AS)
Sabon kocin Barcelona Xavi yana sha'awar sayen dan wasan gaban Algeria Baghdad Bounedjah, mai shekara 29, daga tsohon kulob din Al-Sadd da ke Qatar. (Sport - in Spanish)ho)