An kama mutane uku dangane da fashewar da ta faru a Birtaniya

An wallafa

An kama wasu mutane uku da ake tuhuma da ta'addanci bayan da wani mutum ya mutu sanadin fashewar wata mota a wajen asibitin mata na Liverpool.

Da misalin karfe 11:00 agogon GMT motar - wanda aka ce tasi ce - ta tsaya kuma ta fashe jim kadan bayan haka, in ji 'yan sanda.

An sanar da mutuwar fasinjan motar a wurin da lamarin ya faru kuma har yanzu ba a tantance shi a hukumance ba.

Direban motar ya samu rauni kuma yana murmurewa a asibiti .

Jami'an 'yan sanda masu yaki da ta'addanci sun ce an tsare wasu mutane uku masu shekaru 29, 26 da 21 a Titin Sutcliffe da ke yankin Kensington na birnin.

Sun kara da cewa suna ci gaba da bincike " don gano musabbabin abinda ya janyo fashewar" kuma suna aiki tare da 'yan sandan Merseyside yayin da ake ci gaba da bincike "a cikin sauri".

Jami'an 'yan sanda dauke da makamai sun kai samame a wani gida da ke titin Rutland kusa da Sefton Park, da kuma titin Boaler a Kensington.

'Yan sanda ba su tabbatar da ko samamen na da alaka da fashewar mota a wajan asibitin ba.

Firayim Minista Boris Johnson ya fada a shafinsa na Twitter cewa: "Tunanina yana tare da duk wadanda wannan mummunan lamari ya shafa a Liverpool a yau.

"Ina so in gode wa jami'an agajin gaggawa saboda saurin mayar da martani da kwarewa, da kuma 'yan sanda saboda ci gaba da gudanar da bincike."

Asibitin mata na Liverpool ya ce an hana kai ziyara har sai an ba da sanarwar kuma an mayar da marasa lafiya zuwa wasu asibitocin idan ya yiwu.

Asibitin Mata na Liverpool yana karbar kusan marasa lafiya 50,000 a duk shekara kuma shine asibitin mata mafi girma a Turai.