Abin da 'yan Najeriya ke cewa kan hukuncin da aka yanke wa Abdulrasheed Maina

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 5

Ƴan Najeriya sun yi ta bayyana ra'ayoyinsu a kan hukuncin da wata babbar kotun tarayya a Abuja ta yanke wa tsohon shugaban kwamitin yi wa fanshi garanbawul a ƙasar Abdulrasheed Maina hukunci ɗaurin shekara takwas a gidan yari.

A ranar Litinin 8 ga watan Nuwamba ne Mai Shari'a ya yanke wa Maina hukuncin ɗaurin shekara 61 a gidan yari, amma zai yi zaman shekara takwas ne kawai.

Mai shari'a Abang ya yanke wa Maina wannan hukunci ne kan laifuka 12 da suka haɗa da cin hanci da kuma halasta kuɗaɗen haram.

Tun bayan hukuncin kotun na ranar Litinin ne yan Najeriya suke tabka muhawara kan batun a shafukan sada zumunta na Facebook da Tuwita inda har aka kadammar da maudu'i mai sunansa.

Sannan shi ne mutumin da aka fi neman bayani a kansa a shafin matambayi ba ya ɓata na Google ranar Litinin da Talata.

Da dama na murnar cewa Maina ya girbi abin da ya shuka kuma hukuncin da aka masa ya yi dai-dai.

Sai dai kuma wasu na ganin irin almundahanar da ya tabka da girman laifin da ya aikata kotu ta yi masa sassauci da yawa, kuma ya kamata a ce daurin da zai sha ya fi na shekara takwas.

Har ma akwai masu kwatanta cewa kotu ta daure ɗansa Faisal shekara 14 a gidan yari, to ta yaya za a ce shi kuma zai shafe shekara takwas kacal?

Kuma hotonsa yana murmushi bayan kammala shari'ar shi ma ya janyo muhawara a shafukan sada zumuntar, inda wadanda abin bai yi wa dadi ba ke ganin shi kansa Maina bai zaci zai samu irin wannan garaɓasa a cewarsu.

Ga dai abin da wasu ke cewa a shafin BBC Hausa Facebook:

Nura Dafci Hadejia ya ce: :Wannan Gaskiya ne, kuma ya isa darasi ga masu cinyewa da mallake kayan talakawa, a lokacin da suke giyar mulki.

People nd Power ya ce: "Kai wallahi an rena yan Nigeria, wai mutum ya saci dukiyan al umma an yake masa hukuncin daurin shekara 8, amma har dariya yake, wallahi daga karshe ko prison din ba za su kai shiba, kawai zai gudu zuwa wata ƙasa."

Aliyu Yusuf ya ce: "Dai dai kenan. A ci gaba da zakulo ire-iren su ana daurewa. Amma fa idan bai dawo da kudaden ba tamkar an kashe maciji ne ba a datse kai ba."

Rukayyah Hassan ta ce: "VIP kenan a Kasata. Komai na su daban ne, da talaka ne, hankada shi zaka ga ana yi, sannan expression na fuskar sa zai nuna nadama da damuwa, amma wannan kamar an masa albishir da kujerar shugabancin Nigeria, har waving yake wa mutane cikin farin ciki. Allah ya kyauta."

Wani kuma a shafinsa ga abin da ya ce:

A tuwita kuwa lamarin ya zama muhawara ce tsakanin ƴan arewa da ƴan kudancin ƙasar.

36'KINNIUN @fattylincorn001 ya ce: "Ban ga wani ɗan arewa da ya yi ƙorafi a kan ɗaure Maina ba. Amma ƴan uwana daga kudu da tun daga fitowar rana za su mayar da wannan batun na siyasa."

Souljah @jeffphilips1 "ALlah zai mana maganin duk wani mai shari'a a kotun daukaka kara da ya yi ƙoƙarin sauya hukuncin da babbar kotun tarayya ta yanke wa Maina kamar yadda aka yi na Orji Kalu."

Amma kuma akwai masu ganin cewa ba wani abin ce-ce-ku-ce ba-ne, don a cewarsu akwai wadanda suka aikata laifukan da suka fi na Abdulrasheed Maina kuma har gobe suna nan suna walwalarsu yadda suke so.

A hannu guda kuma hukumar EFCC da ta yi ruwa da tsaki wurin ganin an hukunta Maina ta bayyana hukuncin a matsayin babbar nasara.

A zahiri ba tun yanzu ba ake jin EFCC ta tuhumi masu rike da manyan ofisoshi da almundahana da kudaden al'umma ba.

Amma kuma yan kasar na kokawa kan yadda a karshe kotuna ke jan kafa wurin yanke hukunci, ko kuma su yanke hukuncin da da dama ke ganin ya yi laushi da yawa kamar dai irin na Maina.

Hukuncin shekara 61 zaman gidan kason shekara takwas

Hausawa kan ce 'sharia sabanin hankali, a maimakon bayyana ra'ayinsu game da hukuncin kotun kai Abdulrasheed Maina, wasu yan Najeriyar sun bukaci lauyoyi su yi musu gamsasshen bayani kan dalilin da ya sa Maina zai yi zaman gidan yari na shekara takwas, bayan kotu ta fadi cewa ta yanke masa shekara 61.

Hakan tasa muka tuntubi Barista Audu Bulama Bukarti, don ji daga masanin shariar ko me yasa shekarun da kotu ta furta ke shan ban-ban da abinda mutum zai shafe a tsare?

A cewar Barista Bulama Bukarti "ba sabon abu ba ne kotu ta yanke hukuncin shekaru masu yawa amma kuma ta yi sassauci ga wadanda ta daure, na cewa ta yi masa rangwame ya yi su a lokaci guda idan har akwai laifuka masu wa'adi iri daya."

Ya kara da cewa "idan kuma kotu ta ga dama za ta ce ya yi shekarun ne a wawware, idan ya gama shekarun wannan laifin sai ya fara shekarun laifi na biyu."

A kan haka ya ce kotu ta zabi ta yi wa Abdulrasheed sassaucin yin shekarun ne a dunƙule, wanda ya sa zai shafe shekara takwas a maimaikon 61.

To amma a ra'ayin baristan masu ta da jijiyar wuya kan ce alfarmar da aka yi wa Maina ba ta kamace shi ba suna da gaskiya.

A cewarsa "lura da cewa Abdulrasheed har guduwa ya yi a wannan shari'ar, ya kuma wahalar da shari'a, da kuma yadda a fili take cewa bai tuba ba."

Bugu da kari Barista Bukarti ya ce "Maina ya jefa 'yan fansho da dama cikin uƙuba da ta sa wasu suka rasa haƙƙoƙinsu a karshe ma suka yanke jiki suka fadi suka mutu."

Maina shugaban kwamitin yi wa fansho garanbawul

An nada Maina ne a matsayin shugaban kwamitin garanbawul a harkar fansho a shekarar 2011, da nufin fito da sauye-sauye kan tsarin fansho a Najeriya.

Amma kuma tun kafin a je ko ina a shekarar 2012 aka fara tuhumarsa da almundahanar sama da naira biliyan 100, inda a shekarar 2013 hukumar EFCC ta bayyana cewa tana nemansa ruwa a jallo.

A karshe dai Abdulrasheed Maina ya shiga hannu kuma bayan shafe shekaru ana tirka-tirka kotu ta yanke masa hukuncin zaman gidan yari na shekaru 61, duk da zai yi su ne a cikin shekaru takwas, kuma daga 2019 da aka fara tsare shi.