'Zaben shugabannin PDP nasara ce ga jam'iyyar'

An wallafa

A Najeriya masana kimiyyar siyasa ne suka fara tsokaci kan sakamakon babban taron da jam'iyyar adawa ta PDP, ta gudanar wanda ya tabbatar da Mista Iyochia Ayu a matsayin shugaban babbar jam'iyyar adawar ta Nijeriya.

An dai yi taron cikin lumana ba tare da samun wani yamutsi ba, kamar yadda wasu sukai hasashe tun da fari.

Dakta Abubakar Kari masanin siyasa ne a Najeriyar, ya ce jiga-jigan PDP sun yi wa kansu ƙiyamul laili ne har suka samu nasarar yin babban taron cikin lumana, saboda suna son jam'iyyar ta ci gaba da rayuwa.

''A ganina wannan babban taro da sakamakonsa, babbar nasara ce ga jam'iyyar PDP na gudanar da shi lafiya, alamu sun nuna 'yan jam'iyyar sun rungumi sakamakon zaben. Dama ce ga jam'iyyar ta dinke barakar da ke cikin ta da taka babbar rawa a matsayin babbar jam'iyyar adawa.

Maganar gaskiya ita ce sakamakon wannan zabe na wannan taro ya nuna cewa gwamnonin jam'iyyar PDP sun ma kwace jam'iyyar daga hannun tsofaffi kuma gogaggun 'yan jam'iyyar, wadanda a baya suke ganin cewa su ne masu jam'iyyar. Kusan dukkan wadanda suka ci zaben yaran gwamnoni ne, haka kuma wadanda ba a yi masalaha ba aka yi zabe su ma dai yaran gwamnonin ne.''

Kari ya kara da cewa a yanzu dukkan manyan jam'iyyun Najeriyar PDP da APC, babu wani sashe da ya kai gwamnoni karfin fada aji.

Duk wanda ya ke son wani abu a jam'iyya to dole ne sai ya yi zawarci, da kamun kafa da kuma bi ta kan gwamnoni kafin ya samu.

Sai dai Kari ya ce wannan babbar matsala ce ga dimukradiyya, lamarin ya zama kmar dauki dora.

''Dimukradiyya abin da ta gada shi ne a yi takara, a zo a tsaya zabe, wanda ya ke da goyon baya ya ci, amma yanzu abin da ya ke faruwa shi ne idan kana son wani abu a cikin jam'iyya sai ka yi kamun kafa da goyon bayan gwamnoni ko kuma ka yi hakuri babu abin da za ka samu.''

Yawancin mukaman da aka rantsar a babban taron jam'iyyar PDP dai maslaha aka yi, kuma Dakta Kari y ace ba wannan karon ne kadai aka samu lamari irin haka ba.

Misali siyasar jamhuriya ta hudu haka ta gada, ba a bari a yi takara sai dai ace an yi maslaha. Kuma mafi yawan lokaci idan lamari ya faru irin haka dauki-dora ake yi, kuma tilastawa karfi da yaji ba tare da duba cancanta ba.

Jam'iyyar adawa ta PDP dai ta bakin sabon shugabanta Mista Iyochia Ayu, ta sha alwashin kwace mulki daga hannun jam'iyyar APC mai mulki a zaben shekarar 2023.

Haka kuma, masana na ganin yin babban taron cikin lumana, ba tare da tashin hankali da rarrabuwar kawuna ba, wata alama ce da ken una jam'iyyar da gaske ta ke yi a kokarin farfado da martaba da kimarta da kuma karfinta a idon 'yan Najeriya.