Abin da ya sa aka haramta zancen dare a Rano ta jihar Kano

An wallafa

Mahukuntan karamar hukumar Rano da ke Jihar Kano a Najeriya sun bijiro da wata sabuwar doka da za ta hana zance ko hirar dare tsakanin mata da maza matasa har da zawarawa.

Mahukuntan sun ce sun sanya wannan doka tsakanin masu neman aure a faɗin yankin da zummar kawo tsafta tsakanin matasa.

Wata sanarwa da shugaban karamar hukumar ya fitar Alhaji Dahiru Muhammed Ruwan Kanya, ya ce an dauki matakin ne ganin yada cikin shege ya yawaita da gurbata tarbiyya tsakanin masu zance da sunan neman aure.

Wannan mataki dai ya haifar da mabambanta ra'ayi ko da yake galibin iyayen yara da wasu matasa na ganin hakan ya dace.

Me dokar ta ƙunsa?

Shugaban ƙaramar hukumar Ranon, ya shaida cewa lalacewar tarbiyya ce dalilin bijiro da wannan doka, don haka ya zame musu dole domin tabbatar da kyakkyawan tarbiyya tsakanin matasa da zawarawa a wannan zamanin.

Ya ce daga yanzu iyaye da sauran al'ummar gari za su tabbatar ana zance bisa tsari na zamantakewa da al'adu da addini.

"Mun umarci shugabanni da limamai da sauran hukomomi su kasance masu sa ido a kan yadda ake zance a wannan kasa ta mu, jami'an Hisba da 'yan sanda da sarakuna za su tabbatar da ganin ana bin wannan umarni."

Sannan ya ƙara da cewa jami'ai za su ke yawon sintiri domin tabbatar da cewa kowa ya bi wannan umarni.

Karin wasu labaran da zaku karanta

'Ba zamu lamunci mata na cikin shege ba'

Hakimin Rano kuma Wamban Rano, Alhaji Mannir Tafida Abubakar ya ce da jimawa akwai matsaloli irin na tsarin zancen dare da ke ci musu tuwo a ƙwarya.

Ya ce suna cikin barazanar yawaita samun cikin shege, ga lalacewar mata da maza samari har da zawarawa.

"Suna zance cikin duhu a shafe dare ana lalata da sunan zance.

Iyaye sun sangarta da yara, uba ya wuce ya bar ƴarsa a waje wai tana zance har a bar mata gida ta rufe idan ta gama. Sannan samarin suna daukar mata su kai su inda babu sahun jama'a suna aikata lalata."

Mannir Tafida ya kara da cewa: "Zancen dare ya kasance yana da haɗari a wannan zamanin, don haka duk wanda ya ke neman auren yarinya ya je gidansu da safe ko rana ko yamma.

Sannan idan dole sai dare zai je to ya kasance an ba su damar shiga gida, amma zance a kofar gida mun haramta shi".

Sannan ya ja hankalin iyaye su dau wannan mataki tamkar gyara da cikakken goyon-baya, idan ba haka ba za a dinga hukunta iyayen yara da saurayin da ya je zancen.

Don haka ya zama dole su ba da haɗin kai don rage cikin shege da ake samu a yankin Rano, sannan ya ya kira ga dakatai da limamai wajen sauke nauyin da aka dora musu.

"A rinka tunatar da iyaye kan nauyin da ya rayata wuyansu don kawo karshen wannan matsalar", in ji Tafida.

Me iyaye ke cewa?

Wasu iyaye da BBC ta samu zantawa da su sun ce ba su da ja da wannan doka domin tarbiyya za ta sake inganta.

Wani mahaifi mai suna Shugaban Dan Baba Wanzami Rano, ya ce dama ya kamata a ce nema kar ya ja lokaci, sannan duk ɗan mutunci wajen iyayen yarinya ya kamata yaje ya yi iso a ba shi izini a yi aure.

Ya ce dama tuni abin ya jima yana damunsu don haka sauƙi ya zo a garesu. Kuma duk uba na gari dole zai ji dadin wannan doka.

Abin da matasa ke cewa?

Abubakar Isyaku wani matashi ne da ke zaune a Rano kuma ya shaida mana cewa an kyauta da aka bijiro da wannan doka.

Ya ce dama shi ya fi son hirar rana, kuma baya jin dadin yadda ake kai 11 ko 12 dare da sunan zance tsakanin matasa.

Ita ma wata budurwa, mai suna Maryam Sani Abubakar ta ce wannan doka za ta taimaka wajen kawo karshen maza mayaudara.

Domin galibin maza na tunkararsu da sunan soyayya ko aure amma a karshe sai ka ga yaudara ce a cewarta.

Ta ce galibin mazan da ke zuwa zance dare na "lalube mata da dabaru" don haka wannan doka za ta kawo sauki da yaudarar ƴan mata.