Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ana son kai kayan agaji arewacin Siriya
Babban magatakardar majalisar Dinkin Duniya ya yi kira ga kwamitin tsaro na majalisar ya sabunta aikin kungiyoyin da ke kai kayan agaji arewacin kasar Siriya.
Antonio Guterres ya kuma yi kira ga bangarorin da ke yaki da juna a kasar, su amince da barin hanyar da kayan agaji ta Bab al-Hawa wadda ke tsakanin Siriya da Turkiyya.
Mista Guterres ya ce matukar ba a bude hanyar kai kayan agajin ba, mata da kananan yara zau tagayyara, sakamakon tsananin bukatar abinci da ruwan sha da magani da suke ciki.
Wakiliyar BBC ta ce Amurka da sauran kasashe na son a bar wurin a bude, inda suka ce hanya ce daya tilo da alke kai kayan agaji ga sama da Siriyawa miliyan hudu da suka makale a yankin da 'yan tawaye ke iko da shi a arewacin kasar, wanda a halin yanzu sun dogara ne ga dan abin agajin da suke samu daga ketare wanda dakyar ya ke shiga hannunsu.
A nata bangaren Rasha ta bayyana karara ba ta goyonbayan matakin, tare da cewa ba lallai sai an yi amfani da Bab-al Hawa wajen shiga da kayan ba, za aiya hakan ta birnin Damascus da gwamnati ke iko da shi.
Farar hula da suka makale a yankunan da 'yan tawaye ke iko da su na fuskantar matsaloli da dama, akwai rashin abinci, da asibiti da lalacewar matsugunansu, inda yawanci ke rayuwa a sansanin 'yan gudun hijira a ciki da wajen kasar.