Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Limaman da za su jagoranci Sallar Taraweeh da Tahajjud a Masallacin Harami a bana
Hukumomin Saudiyya sun fitar da jerin sunayen limaman da za su jagoranci sallolin Tarawi da Tuhajjud a Masallacin Harami da ke birnin Makka a lokacin azumin bana.
Shafin intanet na Haramain Sharifain ya bayyana cewa limamai shida ne za su jagoranci gudanar da sallolin a bana.
Ana sa ran za a fara Azumin wannan shekarar a cikin watan Afirilu mai zuwa.
Har wa yau, hukumomin Saudiyya sun ce bana babu wasu limamai da za a gayyato domin limancin sallolin, kamar yadda ake gani a shekarun da suka gabata.
Babban limamin masallacin Ka'abah Sheikh Abdul Rahman al-Sudais na daga cikin limaman da hukumomin suka ce za su yi jagorancin sallolin.
Ga hotunan limaman da za su ja ragamar Sallolin Tarawi da Tuhajjud.