Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
yarjejeniyar nukiliyar Iran: Teheran hana ziyarar ba-zata - IAEA
Shugaban hukumar da ke sa ido kan batutuwan nukiliya Rafael Grossi ya ce Iran ta amince ta kyale jami'an Majalisar Dinkin Duniya masu bincike su ci gaba da ayyukansu na sa ido kan dukkan cibiyoyin da Iran ke amfani da su wajen samar da makamashin nukiliya.
A ranar Talata, wata sabuwar doka za ta fara aiki a Iran da za ta hana jami'an hukumar kai ziyarar bazata har sai Amurka ta dage takunkumin da ta kakaba wa Iran.
Shugaba Biden na son Amurka ta koma aiki da yarjejeniyar nukiliyar Iran ta 2015 wadda tsohon shugaba Trump ya yi watsi da ita.
Sai dai ya ce yana bukatar Iran ta fara mutunta yarjejeniyar kafin ya janye takunkumin da Iran ta kafe sai an cire ma ta kafin ta dauki wani matakin kwance dammara.
Shugaban hukumar ta IAEA Rafael Grossi ya ce za a takaita wa masu bincike na MDD damar shiga wurare a Iran nan gaba, amma ya ce ya kulla wata yarjejeniyar wucin gadi da ta samar da damar ci gaba da tuntubar juna.
Bai bayar da cikakken bayani kan sauye-sauyen da aka samu ba, amma ya ce lamari ne na wucin gadi da ka iya kai wa har nan da wata uku.
Ya kuma ce yarjejeniyar na nufin masu binciken na iya ci gaba da sa ido kan ayyukan da Iran ke gudanarwa na samar da makamashin nukiliya, kana ta ba da damar tattaunawa kai tsaye a siyasance.