Coronavirus: Sama da mutum 30,000 sun kamu cikin kwana ɗaya a Faransa

An wallafa

Hukumomi a Faransa sun tabbatar da kamuwar sama da mutun dubu 30 a cikin kwana daya, duk da kakaba dokar hana yawon dare a birnin Paris da sauran birane takwas.

Mutun 30,621 ne su ka kamu a ranar Alhamis kawai, daga 22,591 a ranar Laraba.

Dama Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta yi gargadin cewa ya zama dole a dauki tsauraran matakan dakile bazuwar annobar cutar korona a karo na biyu.

A ranar Laraba ne Shugaba Emmanuel Macron ya sanar da sabbin matakan kariya, da su ka hada da hana fita a manyan birane kamar Paris da Marseille da Lyon daga karfe 9:00 na dare har zuwa karfe 6:00 na safe har tsawon wata daya.

Mr Macron ya ce sun dauki matakin ne da nufin rage adadin masu kamuwa da cutar a kullum zuwa mutun 3,000.

Ba a Faransa kadai ba, miliyoyi a nahiyar Turai sun tsinci kansu a karkashin sabbin matakai tun bayan kukan kura da cutar Korona ta yia karo na biyu.

A London daga ranar Asabar za a hana haduwar mutane wuri daya koda a cikin gida ne, a wani shirin fito da sabbin matakan dakile Korona masu tsauri sosai a wasu wurare a Ingila.

Har wayau a ranar Alhamis ne kasashen Italiya da Poland da Jamus da ita kanta Faransar su ka shaida adadi mafi yawa na masu kamuwa da cutar Korona a cikin kwana daya.

Kazalika Rasha a karon farko an samu mutuwar mutun 286 a rana daya.

A kan haka WHO ta bukaci gwamnatoci a nahiyar Turai da su tashi tsaye wurin daukar kwararan matakan dakile annobar, ganin cewa ta wuce hasashen da a ka yi a baya na mace macen da a ka yi tsammani.