Mutum 50 sun mutu sakamakon zaftarewar kasa a Dimukradiyyar Kongo

An wallafa

Akalla mutum hamsin ake fargabar sun mutu a Jamhuriyyar Dimukradiyyar Kongo, lokacin da wata mahakar zinare ta dare biyu, a kusa da garin Kamituga da ke gabashin kasar.

Kamfanin dillacin labarai na Reuters ya rawaito wata kungiyar masu hakar ma'adanai ta cikin gida na cewa rushewar ta afku ne a ranar Juma'a.

Magajin garin Bundya Mpila Alexandre, ya ce ruwan sama kamar da bakin kwarya ne ya haifar da aukuwar lamarin.

Ya ce, kungiyoyin masu aikin ceto na kokarin gano wadanda ake kyautata zaton suna raye a karkashin kasa.

Aukuwar irin wannan lamari ta zama ruwan dare a wuraren hakar ma'adanai a Kongo, saboda matakan tsaro da kuma hadarin da aikin ke tattare da shi.

Hotunan da aka watsa a kafafan sada zumunta sun nuna cincirindon mutane sun taru a wurin da lamarin ya faru, rike da shebura da sauran kayan aikin don neman wadanda kila ke raye.

Mahukunta na ci gaba da bayyana damuwa kan yadda jama'a ke bijirewa umarnin hukumomi na bin hanyoyin da suka kamata don neman izini kafin yin irin wannan aiki, amma wasu na dora alhakin hakan a kan talaucin da 'yan kasar ke ciki.