Gyara dokar fyade da satar mutane ya zo kan gaba – Masana

An wallafa

Majalisar dattawan Najeriya ta amince da hukuncin daurin rai da rai ga duk wanda aka kama da laifin garkuwa da mutane a kasar.

A baya dai ana yanke hukuncin daurin shekara 10 ga mutanen da aka kama da laifin.

Haka kuma majalisar ta soke bambancin jinsin maza ko mata kan laifin fyade.

Wannan matsaya da majalisar ta cimma ta biyo bayan tsallake karatu na uku da kudurin ya yi tare da sauya dokar manyan laifuka ta kasar ta 2004.

'Yar majalisa da ke wakiltar jihar Legas ta tsakiya Sanata Oluremi Tinubu ce ta nemi a kara tsaurara dokar da kuma cire banbanci tsakanin jinsi a lokacin yanke hukunci kan fyade.

Kudurin ya cire wa'adin gabatar da kara kan cin zarafi a kasar baki daya.

Idan kudurin ya zama doka, hukuncin cin zarafin zai zama za a iya aiki da shi a ko wanne lokaci.

Abin da masana ke cewa

Wannan yunkuri na majalisar dattawan ya sa masana shari'a a kasar irinsu Barista Abdulhamid Muhammad wanda lauya ne mai zaman kansa yin tsokaci.

Lauya Abdulhamid Muhammad ya bayyana cewa matakin majalisar abu ne mai kyau ganin yadda matsalar fyade da satar mutane ke ci gaba da ta'azzara a Najeriya.

Ya ce dokoki suna tafiya ne da yanayin da kasa ta samu kanta kuma dokokin da aka yi gyare-gyare a kansu sun dauki shekara da shekaru ba a yi wani abu a kansu ba.

"Sannan wadannan laifuffuka da ake ta yi ana nan ana ta yinsu ne, kusan koda yaushe duk minti daya minti biyu sai ka ji maganar wadannan laifuffuka, ko maganar satar mutane ko kuma fyade,"

"Yin hakan ya cancanta a tafi da yadda laifuffukan nan suke tafiya dokokin ma su tafi yadda za su kasance kuma koda an yi wadannan laifuffuka, akwai dokar da za a yi tanadi mai tsauri wanda zai kasance koda masu yin wannan laifin idan suka ji an hukunta mutane da dama a kan wannan, toh suma za su canja yadda rayuwarsu take a kan wadannan al'amuran." kamar yadda lauyan ya shaida wa BBC.

A cewarsa, gyare-gyaren da aka yi wa kundin ya shafi wa'adin da ya kamata a kammala shari'ar fyade ko kuma hukuncin satar mutane wanda "aka ce kada ya wuce wata biyu."

"Yin hakan kuma yana nuna cewa su masu gabatar da kara za su kawo shaidu, su ma wadanda ake tuhuma suma za su kawo shaidu." in ji Barista Abdulhamid.

Lauyan ya kara da cewa a baya, ba a samu kayyadadden lokaci na yanke hukuncin manyan laifuka da suka shafi fyade ko satar mutane amma "a yanzu sai aka sa takaitaccen lokaci wanda ake ganin ya kamata a kammala shari'ar" fyade ko satar mutane.

'Akwai bukatar jihohi su yi koyi da majalisar dattawa'

Lauya Abdulhamid Muhammad ya ce duk da wannan doka ta shafi babban birnin kasar ne suma jihohi ya kamata su dauki darasi daga wannan doka "domin sanar da majalisar tasu ta jihohi domin su yi kokarin shigar da wannan doka ko kuma su yi mata garambawul ko wasu gyare-gyare" da za su yi dai-dai da abin da majalisar dattawa ta yi.

Hanyar hanzarta shari'oin fyade da satar jama'a

A cewar lauyan, samar da kotuna na musamman da za su maida hankali kan sauraron kararrakin fyade da satar jama'a zai taimaka matuka wajen zartar da hukunci cikin sauri.

"Idan aka ce kotu ta musamman ce wannan, ba bu wata shari'a da za ta zo gabata sai wannan shari'ar." in ji Barista Abdulhamid.