'Yan matan Chibok: Ana juyayin cika shekara shida da sace su

Chibok

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Yau ake tunawa da 'yan matan sakandaren da kungiyar Boko Haram ta sace shekara shida a garin Chibok cikin jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya.

Tun bayan sace 'yan matan a shekarar 2014, ake juyayin wannan mummunan al'amari na sace 'yan matan sakandare wanda ya dugunzuma duniya ranar 14 ga watan Afrilun kowace shekara.

BBC ta tattauna da daraktan yada labarai na al'ummar Chibok, Alen Manasseah kan zagayowar wannan rana wanda ya ce har yanzu wasu daga cikin kannensa na hannun 'yan ta-da-kayar-bayan.

Ya ce a duk lokacin da irin wannan rana ta zagayo, iyayen yaran da aka sace da sauran al'ummar Chibok na shiga halin damuwa saboda rashin sanin halin da yaran nasu ke ciki - ko suna raye ko kuma sun mutu.

A cewarsa, babu kwanciyar hankali da zaman lafiya a tsakanin al'ummar yankin musamman iyayen da har yanzu yaransu ke hannun Boko Haram.

"Akwai wadanda saboda damuwa da tunani sun kamu da cutuka, wasu ma sun mutu a cikin iyayen da yaransu ke hannun (Boko Haram),"

"Da fari an samo wasu 21, akwai wadanda suka guda uku, an kuma samo wasu 82 an kawosu gida, suna nan lafiya."

Alen Manasseah ya ce dole ne iyayen da har yanzu yaransu ke hannun Boko Haram su damu saboda abin takaici ne sosai.

Manasseah, wanda ya ce shi ma akwai kannensa 'yan biyu Rebecca da Sarah wadanda har yanzu suke hannun kungiyar ya kara da cewa mahaifiyarsu ta mutu sanadin halin data shiga na rashin yaran nata.

"Suna cikin yara 112 da har yanzu ba a ceto su ba." in ji Manasseah. Ya bayyana cewa sace yaran da aka yi ya katse musu burinsu na zama abin kwatance.

Ya bayyana cewa rashin jin komai daga bangaren gwamnati game da halin da yaran ke ciki abin damuwa ne.

"Tun daga lokacin, ba wanda ke magana da iyayen (yaran), ba wanda ke fadon komai. Ai ya kamata idan an jima a yi musu magana ace har yanzu fa muna kokari ku yi hakuri bamu manta da su ba," a cewarsa.

Bamu gamsu da kokarin gwamnati ba

Chibok

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Daya daga cikin 'yan matan da gwamnatin Najeriya ta kubutar daga hannun Boko Haram a 2016.

Manasseah ya shaida cewa kwata-kwata ba su gamsu da irin rawar da gwamnatin Najeriya take takawa ba don kubutar da 'yan matan daga hannun Boko Haram.

"Saboda me yasa gwamnati ta jira sai ranar da 'yan matan ke cika shekara shida sannan za ta fitar da sanarwa, ai an san cewa suna nan a hannun Boko Haram tun da dadewa,"

"Da a ce suna magana da iyayen nan lokaci zuwa lokaci a tuna da su, idan babba ko shugaban kasa ko na kusa da shi suka bi harkokin yaran nan, ko a ce a tara iyayenssu, a yi musu magana, ga abin da shugaban kasa ya fada ku yi hakuri (ai za su ji dadi).

Amma a manta da su, sai dai a fitar da sanarwa ko kuwa idan an zo wajen wani taro sai a jefa magana,"

"Akwai iyayen a wajen ne? Iyayen guda nawa ne masu talbijin idan ma akwai wuta, nawa ne suke da waya bare su ga sakonni a manhajar whatsapp, nawa suke da intanet bare su ce suna bin shafin Twitter na shugaban kasa,"

"Wadannan mutane ne da suke kauyuka, basu da abubuwan more rayuwa," kamar yadda Alen Manasseah ya bayyana.

Short presentational grey line

Yadda za mu tuna da 'yan matan

A cewar Manasseah, za su gudanar da addu'o'i "a roki Allah ya taimaka, da taimakon masu labarai su sa baki a yi magana da gwamnati su yi abin da za a yi a fitar da su,"

"Saboda an yi sau daya an yi sau biyu, an yarda cewa za a iya yin wani abu a samo sauran 'yan matan ko ma ba duka ba,"

"Dole ne a cikin 112, akwai wadanda har yanzu suna da rai kuma za a iya ceto su," in ji sa.

Short presentational grey line